Yadda gwaggwon biri ke amfani da kiɗa domin aika saƙo

..

Asalin hoton, A SOLDATI

An wallafa

Masana kimiyya sun bayyana cewa gwaggon biri suna da wani salo na kiɗa.

Masu bincike waɗanda suka laƙanci biran a dajin Uganda sun gano cewa biran na tura saƙonni ga junansu idan suna kan bishiya.

Masana kimiyyan sun ce salon kiɗan da biran ke amfani da shi na ba su damar aika saƙo ga wuri mai nisa domin bayyana inda wani yake da kuma aikin da suke yi.

An wallafa sakamakon binciken da masana kimiyyan suka yi a wata mujallar kimiyyar dabbobi.

Dakta Catherine Hobaiter daga Jami'ar St Andrews ta yi bayani kan cewa biran daji suna amfani da manyan rassa na itace inda suke buga su da hannu da ƙafa.

"Idan suka daki icce da ƙarfi, yana yin wata ƙara da ke ratsawa cikin daji," kamar yadda Catherine ta shaida wa BBC.

"Wani lokacin muna gane wa ke kiɗa idan muka ji kiɗa: hanya ce mai kyau da za mu gano wanda muke nema. Idan za mu iya yin haka, na tabbata za su iya."

Kowane namijin chimpanzee, masana kimiyyan sun gano cewa yana amfani da wata hanya ta kiɗa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Suna amfani da wannan sauti da suke yi da baki kuma biran suna kiɗan a wurare da dama.

Mai jagorantar wannan binciken, wadda ɗaliba ce mai digirin digirgir ta yi bayani kan yada su ma wasu bil adama ke amfani da kiɗa domin aika saƙo.

"Na yi mamaki da na gane a cikinsu wa ke kiɗa bayan na shafe makonni kaɗan a cikin daji," in ji ta.

"Yanayin kiɗan na su ya sha bamban da za a iya saurin gane su."

Ms Eleuteri ta alaƙanta wani matashin gwaggon biri wanda masu bincike suka saka wa suna Tristan wanda shi ne kamar jagoran kiɗan a dajin.

"Yana ɗaukar lokaci yana kiɗan kuma za ka iya ganewa daga nesa, za ka iya sanin Tristan ne ke kiɗan.

"Da alama dabbobin suna amfani da salon kiɗan idan suna tafiye-tafiye," in ji Ms Eleuteri.

Ta ƙara da cewa fahimtar yadda gwaggon biran ke kiɗa ta wannan hanyar zai iya bayar da amsa kan wasu abubuwa da ke ɗaure kai: gwaggwon biran daji sun gaishe da kansu idan suka haɗu, amma ba su sallama idan za su rabu a daji.

"Biran ba su sallama idan za su rabu sakamakon za su iya tattaunawa da juna idan ba su kusa," in ji Dakta Hobaiter.