Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Malam Dahir Lawan Mu'az
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Dahir Lawan Mu'az, inda ya fara da bayyana tarihinsa da cewa an haife shi a unguwar Zangon bare-bari, ya tashi a cikin almajirai tare kuma suka fara karatu.
Ya ce ya fara karatun firamare a makarantar Mayanka special Firamare, inda da yamma kuma suke zuwa makarantar Allo.
Malamin ya ci gaba da cewa bayan ya kammala firamare mahaifinsa ya kai shi makarantar Daiba unguwar Rijiyar Lemo domin ya haddace Al-qur'ani daga shekarar 1998 zuwa 2001.
Sannan ya shiga makarantar Kulliyatu Abdullahi Bayero a Kano daga 2001 zuwa 2005, sannan ya wuce jami'ar Bayero ta Kano inda na yi digirinsa na farko a harshen Larabci a shekarar 2011. Sannan kuma da na biyu a harshen Larabci a dai jami'ar ta Bayero a shekarar 2016.
Ya kuma je kasashen Masar da Iran domin yin digiri na uku, amma duka bai samu ya kammala ba saboda wasu matsaloli, sai kuma daga baya ya tafi kasar Italiya inda yanzu haka a can yake kokarin kammala karatun digirinsa na uku.
Surar da ta wahalar da malamin wajen haddar Qur'ani
Malamin ya ce ''duka wuraren da ke kalmomi ko ayoyi masu kamanceceniya sun bani wahala sosai wajen hadda''.
''Ina jin dadin karanta suratul Daha, ina jin dadinta kwarai da gaske, sannan duk wani wuri da Allah ya ke bayar da kissar wani abu, to idan ina karanta shi ina jin dadi'', in ji malamin
Malamin ya shaida mana cewa malamansa na farko su ne malaman da ya fara tasirantuwa da su wadanda ya fara karatun Allo a wajensu, kamar Goni Hadi Goni Idris saboda a wajensa ya fara hada baki, da karatun al-qur'ani, sai kuma malam Abdullahi Uwais wanda shi kuma sai bayan na girma na yi karatu a wajensa, sai kuma malamaina na jami'ar Bayero kaffataninsu
Farin ciki
Malamin ya ce babban abin da ke saka shi farin ciki shi ne yadda ''nake ganin matasa na shiga kokarin neman ilimi na addini da na boko, saboda ci gaban rayuwarsu''.
Abin da ke bata wa malamin rai shi ne zagin magabata
Shawara
Malamin ya ce ''shawarata ga masu amfani da shafukan sada zumunta ita ce idan za su yi, amfani da shafukan, to su yi ta hanyar da ta dace, akwai karatuttukan manyan malamai da dama a shafukan, saboda haka ina kira ga matasa da su yi amfani da wannan wajen sauraron kartuttukan''.
Malamin ya shaida mana cewa Abincin da ya fi so shi ne Doya
Iyali
Malamin ya ce ya yi aure tun shekarar 2014, kuma yana da mata daya da 'ya'ya uku, biyu maza daya mace