Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Muhammad Jamil Alqadiri
Tarihin rayuwarsa
Filinmu na Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Sheikh Muhammad Jamil Alqadiri.
Ya shaida mana cewa sunan mahaifinsa Sulaiman, wanda aka fi sani da Alhaji Sulen Jos, ko Alhaji Sule mai gonjo.
Sunan kakansa Hussaini Muhammad. Malamin ya ce asalin "iyayenmu shi ne garin Gaya a wani kauye da ake kira Hausawa, kuma malaman tsangaya ne, sun yi kaura zuwa wani gari da ake kira Sansani a karamar hukumar Miga da ke jihar Jigawa a yau.
"A can aka haifi kakana da mahaifina daga baya kuma ya dawo Kano inda aka haife ni a unguwar Fagge da ke cikin birni."
Karatun allo
Malamin ya ce ya fara karatu ne a gida, kasancewar "iyayena malamai ne, a makarantar da mahaifinmu ya assasa a gidansa.
Sannan na yi makarantar Malam Adamu mai 'yan makaranta, da sauran makaratun tsangaya.Sannan kuma yi makarantar Muktariyya Islamiyya a unguwar Fagge."
Karatun Boko
Sheikh Alqadiri ya ce ya yi karatun firame a Sabuwar Kofa daga 1984-1990, daga nan "na tafi makarantar addini da Aliya daga 1990- 1996.
"Daga baya na koma harkar karantarwa na koyar a makarantar Masallacin Juma'a na Fagge da Turasul Islam da ke Goron Dutse zuwa 2008.
Malamin ya kara da cewa daga nan ya koma makarantar Koyon Aikin Shari'a ta College of Legal Studies ya yi Diploma a 2003, "na kuma kammala Digiri a 2016 a Ta'ahadud- Dayyib a nan Kano."
Malamaina
Malami na farko shi ne surukina wato mahaifin babbar matata, sai kuma Alhaji Ahmadu Dan fure, a makarantar Tudun Nufawa, da Malam Musa, da Malam Kamilu Adamu wanda ya koya min Tauhidi da Tajwidi, da Larabci.
"Da Malam Hashimu da na koyi Fiqhun Malikiyya da sauran fannonin iimi, da kuma sauran malamai masu dinbim yawa da na amfana da su, in ji Malamin.
Karatun da ya fi wahalar da ni
Sheikh Alqadiri ya ce bai taba samun wani karatu mai wahala a duniya ba, domin akwai wani littafi na kasidar banad -Su'adu, baiti daidai ake biyawa dalibi.
"Amma "ni nakan karanta baiti 11, idan na tsaya ma sai Malam ya ce min na kara."
Ya ce: "Makaranta har sunan ɓarawon karatu suke ce min saboda, yadda nake saurin daukar karatu."
Surar da na fi jin dadin karanta ta
Malamin ya ce Suratul da ya fi jin dadin karantawa ita ce Ahzab, saboda tana karewa da maddul- iwad.
A bangaren hadisi kuwa malamain ya ce ya fi jin dadin hadisin mutum bakwai wadanda Allah zai yi wa inuwa a al'arshi ranar kiyama, saboda an koya mana shi tun muna kanana lokacin da aka yi mana kaciya.
Abin farin ciki
Suna da yawa amma mafi girmansu shi ne samun kaina a gaban hallarar manzon Allah (S.A.W) inda na yi masa wasu baituka a gaban kabarin nasa.
Abin bakin ciki
Malamin ya ce babban abin bakin cikin da ba zai manta da shi ba shi ne yadda "wasu da ga cikin 'yan uwa suka yi kokarin bata alaka ta da Sheikh Qaribulla Nasir Kabara, amma dai daga karshe burinsu bai cika ba."
Abinci
Abincin da na fi so shi ne sarib (a gauraya gurasa da nama) kamar yadda Annabi ya fi so, a abin sha kuma abu mai ruwa-ruwa, sannan kuma da kuma da fura.
Iyali
Ina da mata daya da 'ya'ya takwas, ina fatan Allah ya kawo 'yan bayansu lafiya.
Buri
Babban buri na a a rayuwa shi ne samar da jami'a ta Musulunci, domin cika wa Malam Nasir Kabara burinsa.
Tambayar da aka fi yi min
Mutane sun fi tambayata game da al'amuran gida musamman harkar auratayya.