Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Limamin Kano Farfesa Sani Zahradden
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Farfesa Sheikh Muhammad Sani Zaharaddeen, wanda shi ne babban limamin Jihar Kano.
Liman ya fara karatun Al-Ƙur'ani a garin Ƙiru na Kano a wajen Malam Abdullahi. Kazalika, karatun soro ya kai shi garuruwan Kura da Bebeji, duka a Kano.
Sai dai ya ce biye ya yi, wato ba haddar Ƙur'ani ba a wajen malaman da ya yi karatu a hannunsu.
Daga baya ya shiga kwalejin ilimin harshen Larabci da ke ƙwaryar birnin Kano, inda ya samu shaidar kammala sakandare.
Daga cikin muƙaman da liman ya riƙe har da kwamashinan ilimi na Jihar Kano da kuma shugaban wasu jami'o'i a Najeriya.
Horar da malamai kan haɗin kai
Farfesa Sani Zahraddeen ya ce babbar aƙidarsa ita ce kalmar shahada, kuma ya yi ayyuka da dama wajen haɗa kan malaman ƙungiyoyin addin daban-daban a Kano.
"Lokacin da nake shugabantar Hukumar Shari'a [ta Kano] mukan haɗa tarukan ƙara wa juna ilimi, kuma wannan ya sa malaman sun haɗa kansu," a cewarsa.
"Idan ana ganawa ba za ka ji wani na cewa ni daga Izala nake ko wata bƙungiya ba saboda masalahar Musulmi baki ɗaya.
'Yadda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da jirginmu a a Afghanistan'
Da BBC Hausa ta tambaye shi kan abin baƙinc cikin da ya faru da shi da ba zai manta ba, shehin malamin ya ba da labarin yadda wasu 'yan bindiga da ya kira 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a cikin jirgi.
A cewarsa, lamarin ya faru ne a farkon ƙarnin shekarar hijira ta 1400, inda aka gayyace shi zuwa bikin sabon ƙarni a Jami'ar Peshawar da ke Pakistan.
"'Yan ta'adda sun kai mu Afghanistan, suka tsare mu a cikin jirgi tsawon kwana 12. A nan za kai barci, a nan za ka yi bawali.
"Daga ƙarshe dai Allah kuɓutar da mu, amma da sun ce ƙona jirgin za su yi ko su saka bam. Amma wannan tashin hankali ne babba."
Iyali
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, liman ya ce yana da mata ɗaya, wadda suka shafe shekara 56 tare, kuma suka haifi 'ya'ya takwas.
Sai dai ya ce ɗaya ya rasu daga cikin 'ya'yan.