Matan Indiya da ke fuskantar tsangwama a gidajensu lokacin al'ada

Asalin hoton, Shahbaz Anwar
"A wani lokaci a baya, na saka jadawali a kofar dakina, da ke nuna wa ‘yan gidanmu lokacin al’adata.
Lokacin da mahaifina da kuma kanina suka ga jadawalin da farko, sun ce yin hakan abin kunya ne. Amma a yanzu, sun saba da hakan,’’ a cewar Alfishan.
Ba ita kadai ba. Dubban mata a birnin da take na yin makamancin haka.
Alfishan na rayuwa ne a birnin Meerut da ke arewacin Indiya, mai nisan kilomita 100 daga yammacin birnin Delhi.
A sassa daban-daban na kudancin Asia, al’ada da mata ke yi wata-wata ta zama abin kyama.
A wasu al’ummomin karkara, ana tilasta wa mata da ke jinin al’ada zama a wasu wurare daban da aka kebe da kayan cin abinci daban.
Nuna jadawalin lokacin al’ada
Wadannan al’adu sun zama marassa amfani a tsawon lokaci.
A yanzu, masu gangami na karfafa wa mata gwuiwar cewa da su fito su yi magana kan jadawalin lokacin al’adarsu, da ke nuna lokacin da suke jinin al’ada.
Alfishan ta ce hakan ya taimaka mata matuka.
"Mata na fuskantar matsaloli da dama lokacin yin jinin al’ada. Suna shiga kasala da gajiya da kuma sauran wasu matsaloli.
Amma tun bayan lokacin da na lika jadawalin yin al’ada ta a gida, a yanzu kowa na sane da lokacin da nake yin al’ada.’’
Bayyana lokutan yin al’adarta ya sanya mutane – musamman ma maza –tausaya wa mata

Asalin hoton, Getty Images
Taimakon nisuwa
Ita Alima, labarinta kusan iri daya da na Alfishan. Malamar ta ce bayan bayyana lokutan da take yin jinin al’ada ga dukkan ‘yan uwanta guda bakwai, ta samu taimakon natsuwa ba kamar a baya ba.
"Na san irin matsalolin da mata ma’aikata ke fuskanta lokacin jinin al’ada. Amma idan matan suka fito suka yi magana a kai, muna samun kulawa da ta dace daga gida.
Abu ne mai dadi,’’a cewar Alima yayin tattaunawa da BBC.
Tana rayuwa ne a Meerut, wani birni mai kusan mutum miliyan biyu.
Sama da mata 70 – masu aure da marassa aure ne suka yi rajistar shiga cikin tsarin.
Kamfen din gidauniyar 'Selfie with Daughter'
Shin ta yaya mata suka fara lika jadawalin lokacin yin al’adarsu?
Darektan wata gidauniya mai zaman kanta, 'Selfie with Daughter', Sunil Jaglan, ya ce sun taimaka wajen ganin mata sun saka jadawalin lokutan yin al’adarsu.
Shirin kamfe na al’adar mata a birnin Meerat, ya fara ne a watan Disamban 2021, da lika fastoci a fadin birnin.
"A lokuta da dama, nakan tuna irin matsaloli da mata ke fuskanta lokacin jinin al’ada. Ina ganin ‘yan uwa mata da dama daga gidana na shiga damuwa lokacin al’ada.
"Na yi tunanin cewa ya kamata na yi wani abu a kai. Bayan magana da likitoci, sai na fara wannan kamfe,’’ a cewar Sunil Jaglan.

Asalin hoton, Sunil Jaglan
Kauyukan Nuh da Jind da ke lardin Haryana sune suka fara saka jadawalin lokacin yin jinin al’ada ta mata.
Tun wannan lokaci, kamfe din ya yadu zuwa jihohin Indiya bakwai, inda mata kusan 1,000 suka shiga kamfe din.
'Kalaman da basu dace ba'
Masu aikin sa kai na amfani da wayoyinsu da kafafen intanet da kuma kamfe zuwa gida-gida domin karfafa wa karin mata gwuiwa na ganin sun fito sun yi magana kan lokutan yin jinin al’adarsu.
Suna samun nasarori a wasu lokuta, amma suna gamuwa da turjiya a wasu lokuta.
"Mutane na yin kalamai da ba su dace ba kan mata – har ma kan ‘ya’yansu mata.
A wurare da dama, ana yaga jadawalin lokacin yin al’ada da mata ke likawa ko kuma a hana ‘yan mata saka su kwata-kwata,’’a cewar Jaglan.
Kamar wasu wurare a arewacin Indiya, birnin Meerut na da ra’ayin rikau wanda hakan ke zama wahala ga mata su zauna a gidajensu lokacin yin al’ada.
Gidauniyar ta samu goyon bayan shugabannin kungiyoyin addini domin saukaka musu yin kamfe din.
Matsi daga gidajen manyan iyalai

Asalin hoton, Shahbaz Anwar
Tsarin zamantakewa ya taka rawa wajen saka shirin na kamfe yin tafiyar hawainiya. Aaliya matar aure ce da ke rayuwa cikin babban gida – hakan ya kara mata kalubale.
"Baya ga mijina da surukina da kuma kanin mijina da kuma sauran ‘yan uwa maza, dukkansu suna kawo min ziyara.
Don haka, lokacin da na fara jin batun jadawalin lokacin al’ada, na dauka hakan ba zai yu ba a gidana. ‘’
Aaliya ta samu goyon bayan mijinta kan batun na saka jadawalin lokacin al’ada, inda ya kuma tabbata cewa mahaifiyarsa ma ta aminta da hakan.
A yanzu, Aaliya na samun karin goyon baya daga sauran mutanen gidansu lokacin da take yin al’ada.
’Ba mu da kudin sayan auduga’
Wata da ta shiga tsarin na saka jadawalin lokacin al’ada mai suna Manisha – ta ce hakan ya sanya mata tattauna batun al’ada da ‘yan uwansu maza ba tare da kokonto ba.
"Wannan abu ya shafi lafiyarmu. Ya kamata kowaye a cikin iyalai su san matsalolinmu lokacin al’ada.
"Mata suna saurin fushi da kuma son yin musu lokacin al’ada. Bayan mutane sun gano cewa hakan ya shafi lafiyar matan, sun fara nuna tausayi kansu.’’

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da gwamnatin Indiya ta wallafa a 2019, ya nuna cewa yawancin ‘yan mata da kuma mata a Indiya har yanzu suna amfani da hanyoyin kariya marassa tsafta a lokutan al’ada, kamar tsoffin tufafi.
Yawancinsu ba su da damar sayen auduga saboda talauci.
A shekarun baya-bayan nan, audugar da ake samarwa a cikin gida ta saukaka wa matan wadanda ba su da damar saye saboda talauci.
Sai dai camfe-camfe da aka alakanta da al’ada, sun hana mata zuwa shaguna don sayan abubuwan kariya lokacin al’ada musamman ma auduga.
'Jinin al’ada ba abin kunya ba ne'
A tsawon shekaru, mahaifiyar Alfishan ta kasance tana saya mata auduga, sannan ta boye ta cikin wata bakar jaka.
"Na kasance ina jin kunyar zuwa sayen auduga wajen wani mai shago, amma a yanzu,da kaina nake zuwa saye. Hakan ba abin kunya ba ne,’’ a cewar Alfishan.
Wadanda aka dama da su, sun yi kankanta domin kawo wani canji a cikin al’umma.
Abin da ya bai wa Jaglan kwarin guiwa shi ne ganin karuwar maza da ke ba wa matansu kulawa lokacin al’ada kamar Zubair Ahmed.
Mutumin wanda mai sana’ar yin aski ne, na karfafa wa matarsa gwuiwa wajen ganin ta saka jadawalin na lokutan al’ada.
Ya fada mata cewa za ta iya lika jawadalin a kan kowaxe kofa a gidansu.
Zubair na da sakon goyon baya ga maza da mata kamarsa.
"Bai kamata a tilasta wa mata yin aiki ba lokacin al’ada. Kada mata su damu kan me mutane za su ce a kan al’ada,’’











