Wasu zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a sassa daban-daban na duniya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, 'Yan ƙasar Uganda kenan ranar Litinin a lokacin bikin rawar Agwara da ake gudanarwa shekara-shekara a birnin Kampala. Bikin na ɗaya daga cikin tsofaffin bukukuwan al'ada a nahiyar Afirka
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafar Ghana kenan ranar Juma'a a birnin Doha na Qatar gabanin fara gasar cin Kofin Duniya ta 2022
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Wasu 'yan Najeriya a lokacin da suke ƙoƙarin tseratar da jakankuna bayan da gobara ta tashi a masana'antar yin jakankuna ta Yunuo da ke jihar Ogun a kudu maso yammacin kasar
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Nan kuma mahalarta taron sauyin yanayi ne na COP27 ke rawa domin nuna murna ranar Talata. Taron na gudana ne a Sharm El-Sheikh da nufin aiwatar da tsare-tsare domin kare muhalli
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Su ma waɗannan mahalarta taron ne ke ɗaukar hotuna a wajen taron
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, An gudanar da bikin nuna kayan ƙawa na Afirka a birnin Kibera na kasar Kenya ranar Juma'a.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Asiya Yakub kenan wadda ita ma ta halarci bikin da aka gudanar a ranar ta Juma'a
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Hiwot Yirga sarauniyar kyau ta Ethiopia a lokacin da ta wakilci ƙasarta a babbar gasar 'Sarauniyar kyau ta duniya' da aka shirya a ƙasar Philippiness ranar Litinin. Babbar gasa ce ta duniya wadda za ta mayar da hankali wajen wayar da kan al'uma game da kare muhalli
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Sarauniyar Kyau ta Najeriya Esther Ajayi, na daga cikin waɗanda suke fatan lashe gasar. Wadda duk ta lashe wannan gasa ita ce za ta zama jakadiyar kare muhalli ta duniya
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Dakarun Kenya suna fareti gabanin ɗaukarsu zuwa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo domin aikin wanzar da zaman lafiya
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Matasan Sudan ke zanga-zangar neman adalci ga waɗanda aka kashe a lokacin juyin mulkin ƙasar a shekarar da ta gabata