Za a fara saurarar ƙarar Alves a cikin Fabrairu kan zargin fyade

Asalin hoton, Getty Images
Za a fara sauraren karar da aka shigar kan tsohon dan wasan tawagar Brazil da Barcelona, Dani Alves kan zargin fyade daga ranar 5 zuwa 7 ga watan Fabrairun 2024.
Alves, mai shekara 40 yana garkame a kurkuku, tun bayan da aka tsare shi a cikin watan Janairu kan zargin cin zarafin wata mata a wani gidan rawa a Barcelona a bara.
Ya yi bayanin cewa da amincewarta ya sadu da ita, bayan da tun farko ya musanta cewar ya yi lalata da ita.
Masu shigar da kara a Sifaniya na neman a daure Alves shekara tara a gidan yari.
Haka kuma masu shigar da karar na fatan kotu za ta aike masa da oda yin tsakaninsa da matar, sannan ya biya matar tarar Yuro 150,000
Cikin watan Agusta wata kotu ta tuhumi dan wasan daga nan ta yanke shawarar cewar tana da hujjojin da yawa da za ta daure shi a kurkuku.
Alves ya buga wa Brazil wasa 126, inda ya buga wa kasar gasar cin kofin duniya a Qatar a 2022, sai dai kungiyarsa ta Mexico Club UNAM ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu tun bayan da aka tsare dan wasan.
A kasar Sifaniya zargin fyade idan ya tabbata, bayan zaman kotu za a iya yanke hukuncin zaman yari daga shekara hudu zuwa 15.











