Lille ta yi wa Yoro barazana don ya tafi Man Utd, Arsenal za ta haƙura da Guehi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Lille ta yi barazanar ƙin sanya ɗan bayan Faransa, Leny Yoro, mai shekara 18, a wasanni a shekararsa ta ƙarshe a ƙungiyar idan ya ƙi yarda Manchester United ta saye shi. (Marca)

Liverpool ta rage sha'awarta a kan Yoro bayan da matashin ɗan wasan ya buƙaci samun tabbacin sanya shi a wasa akai-akai a Anfield. (Athletic)

Tottenham na neman shiga gaban Fulham wajen sayen ɗan wasan tsakiya na Manchester United Scott McTominay ɗan Scotland (Sun)

Arsenal na shirin haƙura da ɗan bayan Ingila Marc Guehi saboda Crystal Palace ta tsuga masa kuɗi har sama da dala miliyan 70. (Mirror), external

Ana sa ran Brentford ta rage farashin da ta sanya zuwa ƙasa da fam miliyan 50 a kan ɗan gabanta Ivan Toney, ɗan Ingila mai shekara 28, saboda ƙungiyoyi abokan hamayya ba su nuna sha'awarsu a kan ɗan wasan ba. (Sun)

Har yanzu Manchester United na sha'awar ɗan wasan tsakiya na Paris St-Germain, Manuel Ugarte, na Uruguay mai shekara 23. (Sky Sports)

Tottenham ta kasance tana tuntuɓar wakilan ɗan wasan gaba na Kanada Jonathan David, mai shekara 24, kafin ta gabatar da ɓukatar wa Lille buƙatar sayensa. (Football Insider)

QPR na sha'awar ɗan wasan gaba na gefe na New Zealand, wanda a da yake Bayern Munich Sarpreet Singh, mai shekara 25. (Football Insider)

An buƙaci ɗan bayan Italiya Riccardo Calafiori, mai shekara 22, ya je wasannin shirin tunkarar sabuwar kaka tare da Bologna, yayin da Arsenal ke ƙoƙarin cimma matsaya a kan farashinsa. (Evening Standard)

Rahotanni sun ce Chelsea ta tuntuɓi RC Lens domin ta sayi matashin ɗan wasanta na gaba Elye Wahi mai shekara 21, bayan da Blues ta yi rashin nasarar sayen ɗan Faransan a bazarar bara (L'Equipe)

Rahotanni na cewa Lyon na shirin bayyana nasarar sayen matashin ɗan wasan gaba na Southampton Alejandro Gomes Rodriguez mai shekara 16 bayan da ɗan tawagar Ingila ta 'yan ƙasa da shekara 16 ya ƙulla yarjejeniyar shekara uku da ƙungiyar. (Fabrizio Romano)

Bayanai sun nuna cewa Chelsea ta tuntuɓi Paris St-Germain a game da ɗan gabanta na Portugal Goncalo Ramos, mai shekara 23, da ɗan gaban Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 25, domin maye gurbin Romelu Lukaku idan ya tafi. (HITC)