Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aubameyang ya koma Saudiyya
Tsohon ɗan wasan Arsenal da Chelsea, Pierre-Emerick Aubameyang ya kammala komawa ƙungiyar Al Qadsiah da ke Saudiyya daga Marseille.
Aubameyang, mai shekaru 35, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da ƙungiyar, wadda ta samu daukaka zuwa babbar gasar saudiyya, Saudi Pro League a kakar wasan da ta gabata.
A sabon kulob ɗin nasa, kyaftin ɗin Gabon zai taka leda tare da tsohon ɗan wasan baya na Real Madrid Nacho, wanda ya kammala komawa ƙungiyar a watan jiya.
Aubameyang ya yi wasa a Arsenal da Chelsea na jimillan kakar wasa 6 inda ya zura ƙwallaye 69 sannan ya taimaka aka zura 16 a wasanni 143 da ya bugawa ƙungiyoyin biyu.