Wa zai lashe kyautar Ballon d'Or ta 2024?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A ranar 4 ga Satumba za a sanar da jerin waɗanda za su yi takarar zama gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya - inda za a yi la'akari da kakar wasa ta 2023-24 tare da kuma manyan gasa da aka gudanar a bazara.

Yayin da Vinicius Jr da Jude Bellingham na Real Madrid suka kasa lashe gasar cin kofin nahiya da suka buga da Brazil da Ingila, hakan na nufin kambun ya zama na mai rabo ka ɗauka.

Ga ƴan wasa shida da ake sa ran ɗayan su zai iya yin nasara a bikin da za a yi a ranar 28 ga watan Oktoba a birnin Paris:

Vinicius Jr (Real Madrid da Brazil)

An daɗe ana alaƙanta ɗan wasan gaban Real Madrid Vinicius, mai shekara 24, da lashe kyautar Ballon d’Or bayan ya taimaka wa ƙungiyarsa ta lashe gasar La Liga da kuma gasar zakarun Turai.

Ya kasance ɗan wasan da ya fi zura wa Real Madrid ƙwallo a raga a kakar wasa ta bana inda ya zura ƙwallo 24 sannan ya taimaka aka zura 11.

Samun nasarar lashe gasar Copa America da Brazil ce za ta kusan tabbatar da nasararsa na lashe kyautar - amma Uruguay ta yi waje da su a bugun fanariti, a wasan da Vinicius bai buga ba saboda dakatarwar da aka yi masa bayan karɓar katin gargaɗi biyu a matakin rukuni.

Ɗan Brazil na ƙarshe da ya lashe kyautar Ballon d’Or shi ne Kaka a shekara ta 2007, tun lokacin Neymar ne kawai ya ji kamshin ta da ya ƙare cikin ukun farko.

Rawar da ɗan wasan ya taka a kakar da ta wuce:

Wasanni: 49.

Ƙwallaye da ya ci: 26.

Wanda ya taimaka: 11.

Kofuna da ya lashe: La Liga, Champions League, Spanish Super Cup.

Rodri (Manchester City da Sifaniya)

Ɗan wasan tsakiya Rodri, mai shekara 28, ya yi rashin nasara a wasa ɗaya ne kacal a duk kakar wasan da ta gabata a kulob ɗin da kuma ƙasarsa (ban da bugun fanareti) - wasan ƙarshe na cin kofin FA da Manchester United.

Ya yi nasarar lashe kofuna uku a kakar wasan da Manchester City, sa'annan ya ƙara da Euro 2024 a bazara da Sifaniya.

Ya ji rauni ne a lokacin hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Turai da Ingila, amma ya riga ya yi abin da ya dace don a naɗa shi ɗan wasan da ya fi fice a gasar.

Babu wani ɗan wasan Manchester City da ya taɓa lashe kyautar Ballon d'Or a lokacin da yake taka leda a kulob ɗin.

Rawar da ya taka a bana:

Wasanni: 63.

Ƙwallaye da ya ci: 12.

Wanda ya taimaka: 14.

Kofuna da ya lashe: Premier League, Uefa Super Cup, Club World Cup, Euro 2024.

Jude Bellingham (Real Madrid da Ingila)

Ɗan wasan tsakiya na Ingila Bellingham, mai shekara 21, taka rawar gani a kakar wasansa ta farko a Real Madrid bayan ya bar Borussia Dortmund a bara.

Ya ci kwallaye 23 - ciki har da guda biyu da jefa wa Barcelona a gida da waje a gasar La Liga - ya kuma an zura 13 yayin da suka lashe babbar gasar Sifaniya da gasar zakarun Turai.

Ya kuma nuna bajintarsa a gasar Euro 2024 inda ya farke ƙwallon da aka ci Ingila a ƙarin lokaci a wasan zagayen ƴan 16 da suka buga da Slovakia.

Da ya yi zaburar da Ingila ta yi nasara a kan Sifaniya a wasan ƙarshen gasar, mai yiwuwa ya zama ɗan wasan Ingila da zai lashe kyautar Ballon d’Or na farko tun bayan Michael Owen a shakarar 2001.

Rawar da ya taka a bana:

Wasanni: 54.

Ƙwallaye da ya ci: 27.

Wanda ya taimaka: 16.

Kofuna da ya lashe: La Liga, Champions League, Spanish Super Cup.

Dani Carvajal (Real Madrid da Sifaniya)

Ba a taɓa tsammanin ɗan wasan baya na gefen dama Carvajal, mai shekara 32, zai iya fitowa cikin ƴan takarar Ballon d'Or ba, amma ya zama ɗaya daga cikin mutane 12 da suka buga kuma suka lashe wasan ƙarshe a gasar zakarun Turai da na nahiyar Turai (EURO) a kakar wasa guda.

Ya zura ƙwallon farko da Real Madrid ta ci a wasan ƙarshe na cin kofin zakarun Turai da suka doke Borussia Dortmund - sannan kuma ya ci wa Sifaniya ƙwallo a gasar Euro 2024 da ta doke Croatia a matakin rukuni.

Idan har ya yi nasara Carvajal zai zama ɗan wasan baya na gefen dama na farko da ya lashe kyautar Ballon d'Or.

Rawar da ya taka a bana:

Wasanni: 54.

Ƙwallaye da ya ci: 7.

Wanda ya taimaka: 8.

Kofuna da ya lashe: La Liga, Champions League, Spanish Super Cup, Euro 2024.

Lamine Yamal (Barcelona da Sifaniya)

Ɗan wasan gefe na Barcelona Yamal ya riga ya yi kakar wasa mai ban sha'awa musamman ganin cewa shekarunsa 16, yayin da ya buga wasanni 50 a kulob ɗin

Hakan ya sanya shi zama ɗan wasa mai mafi ƙarancin shekaru da ya buga wasanni 50 a Barcelona.

Ƙwallaye guda huɗu da ya taimaka a zura a gasar Euro 2024 a Jamus sun yi daidai da adadi mafi yawa a gasar cin kofin nahiyar Turai - kuma ya zura ƙwallo mai ban sha'awa a wasan da suka doke Faransa a matakin kusa da na ƙarshe.

Ya kasance ɗan wasa mai mafi ƙarancin shekaru, wanda ya zura ƙwallo a raga kuma ya yi nasarar lashe gasar cin kofin nahiyar Turai - ya cika shekara 17 kwana ɗaya kafin wasan ƙarshen gasar - shi ne aka naɗa gwarzon matashin ɗan wasa a gasar.

Shahararren ɗan wasan Brazil Ronaldo, mai shekara 21, shi ne matashin ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar 1997.

Bajintarsa a wannan kakar:

Wasanni: 64.

Ƙwallaye da ya ci: 10.

Wanda ya taimaka: 14.

Kofuna da ya lashe: Euro 2024.

Lionel Messi (Inter Miami da Argentina)

Messi, mai shekara 37, shi ne ɗan wasan da ya fi samun nasara a tarihin Ballon d’Or, inda ya lashe sau takwas – ciki har da shekarar da ta gabata, sakamakon yadda ya jagoranci Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya.

Har yanzu yana cikin waɗanda ake tunanin zai iya lashe kyautar amma zai zama abin mamaki idan ya yi nasara.

Ya zura ƙwallo ɗaya kacal a gasar cin kofin Copa America da Argentina ta yi lashe a bana, a karawar da suka yi da Canada a wasan dab da na kusa da na ƙarshe, ya ji rauni a wasan ƙarshe, inda da yawa ke ganin bai taɓuka abin a zo a gani ba.

Messi bai ci kofi ko ɗaya da Inter Miami ba a kakar wasan da ta gabata.

Rawar da ya taka a bana:

Wasanni: 39.

Ƙwallaye da ya ci: 28.

Wanda ya taimaka: 17.

Kofuna da ya lashe: Copa America 2024.