An raba maki tsakanin Aston Villa da Man United a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa da Manchester United sun tashi 0-0 a wasan mako na bakwai a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Villa Park.
A bara a irn wannan lokacin, United ce ta ci Aston Villa 2-1 a babbar gasar tamaula ta Ingila, tun farko United ta ci 3-2 a Old Trafford.
A wasa 26 da Aston Villa ta karɓi bakuncin United, sau ɗaya ne ta ci 3-1 a karon farko da Unai Emery ya karɓi aikin jan ragamar Villa a Nuwambar 2022.
Da wannan sakamakon Villa ta haɗa maki 14 a wasa bakwai, bayan nasara huɗu da canjaras biyu aka doke ta karawa ɗaya.
Ita kuwa United maki takwas ta samu a karawa bakwai, bayan nasara biyu da canjaras biyu aka doke ta fafatawa uku.
United za ta buga wasan gaba a Premier League ranar Asabar 19 ga watan Oktoba, inda za ta fafata da Brentford a Old Trafford.
Daga nan za ta je gidan Fenerbahce a Europa League ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba.
Ita kuwa Villa za ta je gidan Fulham a wasan mako na takwas a Premier League ranar Asabar 19 ga watan Oktoba.
Sannan ta karɓi bakuncin Bologna a wasa na uku a Champions League ranar Talata 22 ga watan Oktoba.










