Ba zan yi gaggawar saka De Bruyne a wasa ba - Guardiola

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya ce ba zai yi gaggawar saka Kevin De Bruyne a wasan Manchester City ba, bayan jinya da ya yi.
Ɗan ƙwallon tawagar Belgium ya yi zaman benci ranar Asabar a gasar Premier League da Bournemouth ta doke City 2-1 a Vitality.
Guardiola ya ce bayan jinyar mako bakwai da De Bruyne ya yi, yana son ya tabbatar da cewar ɗan wasan ya murmure sarai kafin ya saka shi a wasan City.
Ya kara da cewar a bara ya yi jinyar wata biyar, wanda ya koma buga wa City wasanni da kafar dama, har ya bayar da gudunmuwar da ƙungiyar ta taka rawar gani.
City mai rike da Premier League ba ta kan ganiya tun bayan da Rodri ya fara jinya, wanda ya ji rauni a karawar da suka tashi 2-2 da Arsenal a Etihad.
Tun kafin wasan da City ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth ranar Asabar, tuni kuma Tottenham ta yi waje da ita a Carabao Cup na bana.
Ranar Talata City za ta je Sporting a Champions League daga nan ta kece raini a gidan Brighton a Premier League ranar Asabar 9 ga watan Nuwamba.
City tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool mai jan ragama, wadda ta doke Brighton a Anfield a karshen mako.











