Real ta kai kwata fainal da ƙyar da gumin goshi a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a Champions League, bayan da ta fitar da Atletico Madrid a bugun fenariti da cin 4-2 ranar Laraba.
Ɗan wasan Atletico, Julian Alvarez ya ci bugun daga kai sai mai tsaron raga, amma aka soke da cewar lokacin da ya zame ɗaya kafar ta taɓa ƙwallo sannan ya kara buga wa da ɗayan.
Kenan Real Madrid za ta buga kwata fainal da Arsenal a watan gobe, kuma ƙungiyar Sifaniya na fatan lashe Champions League na bana na 16 jimilla.
Atletico ce ta ci ƙwallo a dakika 27 ta hannun Conor Gallagher ranar Laraba, bayan da Real ta yi nasara a wasan farko 2-1 a makon jiya a Santiago Bernabeu.
Hakan ya sa ta kai ga bugun fenariti, kenan kowacce ta ci ƙwallo 2-2 gida da waje da suka fafata, kuma ukun farko kowa ya zura ƙwallo a cikin raga.
Daga nan tsohon ɗan wasan Manchester City, Alvarez ya buga fenariti ta kuma faɗa raga, kuma alkalin wasa ya karɓi cin.
Daga baya aka je VAR, wadda ta fayyace lokacin da ɗan wasan zai zame ya taɓa ƙwallon sannan ya sake bugawa a karo na biyu, sai aka soke cin da ya yi.
Shi kuwa Fede Valverde ya zura ƙwallon da ya buga a raga, hakan ya sa Real na cin 3-1, koda yake golan Atletico, Jan Oblak ya tare fenaritin Lucas Valquez, sai kuma dan wasan Atletico, Marcos Llorente ya buga ƙwallo ya doki turke.
Daga karshe Antonio Rudiger ya ci wanda ya buga aka tashi daga bugun fenaritin Real Madrid ta yi nasara da 4-2.
Rabon da Atletico ta yi rashin nasara a gida a zagayen kwata fainal tun rashin nasara a hannun Ajax a 1997.
Tun kan tashi daga karawar aka sauya Vinicius Junior, wanda a cikin wasa ya buga fenariti, amma ta yi saman raga saura minti 20 lokaci ya cika.
Ƴan wasan Real Madrid:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy, Asencio da kuma Jacobo.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Chema.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim da kuma Gonzalo.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X










