Liverpool na duba ko ya kamata ta yi zawarcin Chiesa na Juventus

Federico Chiesa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool na duba ko ya kamata ta yi zawarcin ɗan wasan Juventus, Federico Chiesa.

Mai shekara 26 yana cikin tawagar Italiya a Euro 2024, yana da sauran kwantiragin kaka ɗaya da ya rage masa a Juventus.

Sai dai ba a bayyana sunansa ba cikin waɗanda suka buga wa Juventus wasa da Como da wanda ta kara da Hellas Verona ranar Litinin.

Har yanzu Liverpool ba ta ɗauki ɗan wasa ba a kakar nan, amma yanzu dai ta tabbata tana duba ko ya kamata ta ɗauki ɗan ƙwallon Juventus, Chiesa.

Tun farko Liverpool ta tuntuɓi mai tsaron ragar Valencia, Giorgi Mamardashvili daga baya batun bai kammala ba.

Liverpool tana buga kakar bana da sabon koci, Arne Slot, wanda ya maye gurbin Jurgen Klopp, wanda ya yi aiki a Anfield kaka tara.

Haka kuma Liverpool ta yi kokarin sayen ɗan wasan tawagar Sifaniya, Martin Zubimendi, wanda ya zaɓi ci gaba da taka leda a Real Sociedad.

Chiesa ya koma Juventus daga Fiorentina a 2020 kan £54m.

Ya buga wa ƙungiyar karawa 131, yana cikin tawagar Italiya da ta lashe Euro 2020, amma yawan jinya ta sa baya buga wasanni da yawa.