Me amincewa da kafa ƙasar Falasɗinawa ke nufi?

...

Asalin hoton, EPA

    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC diplomatic correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinu a watan Satumba idan har Isra'ila ba ta cika wasu sharudda – ciki har da amincewa da tsagaita wuta a Gaza da kuma farfaɗo da mafita ta ƙasashe biyu ba.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu dai ya mayar da martani cikin fushi, yana mai cewa wannan matsayi na Birtaniya "ya goyi bayan baƙin 'ta'addancin' Hamas ne kawai."

Idan amincewar da Birtaniya ke shirin yi ta tabbata, me hakan ke nufi, kuma me zai sauya?

Me amincewa da kafa ƙasar Falasɗinawa ke nufi?

Falasɗinu ƙasa ce wadda akwai ta amma kuma a hukumance babu ita.

Wasu ƙasashe sun amince da ita matsayin ƙasa, tana da ofisoshin jakadanci a waje, kuma tana da ƴan wasanni da ke shiga gasa irin su Olympics.

Amma saboda rikicin da Falasɗinawa ke fama da shi da Isra'ila tsawon shekaru, Falasɗinu ba ta da iyakoki da aka amince da su a duniya, ba ta da babban birni a hukumance kuma ba ta da rundunar soji.

Hukumar Falasɗinawa da aka kafa a shekarun 1990 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan wanda ke ƙarƙashin ikon Isra'ila ba ta da cikakken iko da mutanenta da kuma ƙasarta.

Gaza, inda Isra'ila ita ma ta mamaye na cikin wani mummunan yanayi na yaƙi da ke ci gaba da hallaka rayuka da dukiyoyi.

Amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu zai fi zama wata alama ta ɗabi'a da siyasa. Zai nuna goyon baya mai ƙarfi, amma ba lallai ya kawo sauyi kai tsaye ba.

Sai dai wannan alamar tana da ƙarfi sosai. Kamar yadda ministan harkokin wajen Birtaniya, David Lammy, ya bayyana a jawabin da ya yi a Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Talata, "Birtaniya na da wani nauyi na musamman na tallafa wa mafita ta ƙasashe biyu."

Sojojin Birtaniya yayin da suke sauke tutar Union domin kawo ƙarshen mulkin mallakar Birtaniya a Falasdinu a shekarar 1948.

Asalin hoton, Bettmann via Getty Images

Bayanan hoto, Sojojin Birtaniya yayin da suke sauke tutar Union domin kawo ƙarshen mulkin mallakar Birtaniya a Falasdinu a shekarar 1948.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

David Lammy ya ambaci Sanarwar Balfour ta 1917, wacce tsohon ministan harkokin wajen Birtaniya, Arthur Balfour, ya sanya wa hannu, inda Birtaniya ta nuna goyon bayanta ga kafa ƙasar Yahudawa a Falasɗinu. Amma, a cewarsa, sanarwar ta kuma yi alƙawarin cewa hakan ba zai tauye haƙƙin addini da na farar hula na sauran al'ummomin da ba Yahudawa ba a Falasɗinu.

Masu goyon bayan Isra'ila a lokacin sun ce sanarwar ba ta ambaci Falasɗinawa kai tsaye ko haƙƙinsu na kafa ƙasa ba.

Ƙasar Falasɗinu da Birtaniya ta mulka daga shekarar 1922 zuwa 1948 ta daɗe ana kallonta a matsayin wata matsala da ba a kammala ba a matakin ƙasashen duniya.

Isra'ila ta samu 'yanci a shekarar 1948, amma ƙoƙarin kafa ƙasar Falasɗinu bai taba kai wa ga nasara ba.

Kodayake ana yawan ambaton mafita ta ƙasashe biyu — wato kafa Falasɗinu kusa da Isra'ila a cikin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Urushalima da Gaza — amma wannan mafita ta zama kamar kawai magana ce, ganin yadda Isra'ila ke ci gaba da mamaye manyan yankunan da doka ta ƙasashen duniya ta haramta.

Ƙasashe nawa suka amince da kafa ƙasar Falasɗinawa?

A yanzu haka ƙasashen 147 ne suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasar a cikin mambobi 193 na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A Majalisar Ɗinkin Duniya, Falasɗinu ta kasance ƙasa ƴar kallo, wato tana iya halartar taruka amma ba ta da damar kaɗa ƙuri'a.

Faransa ta yi alƙawarin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa nan gaba kaɗan, kuma idan Birtaniya ma ta bi sahu, Falasɗinu za ta samu goyon bayan ƙasashe huɗu daga cikin biyar da ke da matsayi na dindindin a kwamitin tsaro na MDD — wato China da Rasha da Faransa da Birtaniya da kuma Amurka, wacce ke da alaƙa mai ƙarfi da Isra'ila.

Tun daga tsakiyar shekarun 1990, Amurka ta amince da Gwamnatin Falasɗinu da Mahmoud Abbas ke jagoranta, amma har yanzu ba ta amince da ita a matsayin ƙasa cikakkiya ba.

Wasu shugabannin Amurka sun nuna goyon bayansu ga kafa ƙasar Falasɗinu a nan gaba, amma Donald Trump ba ya daga cikinsu.

A halin yanzu dai, Amurka ta fi nuna goyon bayanta ga Isra'ila.

Idan babu goyon bayan Amurka, wadda ke da alaƙa mai ƙarfi da Isra'ila, zai matuƙar wahala a samu yarjejeniyar zaman lafiya da za ta haifar da ƙasashe biyu.

Jerin ƙasashen da suka amince da kafa ƙasar Falasɗinawa

  • Afghanistan 16 Nuwamba 1988
  • Albania 17 Nuwamba 1988
  • Algeria 15 Nuwamba 1988
  • Angola 06 Disamba 1988
  • Antigua & Barbuda 22 Satumba 2011
  • Argentina 06 Disamba 2010
  • Armenia 21 Yuni 2024
  • Azerbaijan 15 Afrilu1992
  • Bahrain 15 Nuwamba 1988
  • Bangladesh16 Nuwamba 1988
  • Barbados 19 Afrilu 2024
  • Belarus 19 Nuwamba 1988
  • Belize 09 Satumba 2011
  • Benin 12 Mayu 1989
  • Bhutan 25 Disamba 1988
  • Bolivia 17 Disamba 2010
  • Bosnia-Herzegovina 27 Mayu 1992
  • Botswana 19 Disamba 1988
  • Brazil 03 Disamba 2011
  • Brunei 17 Nuwamba 1988
  • Bulgaria 25 Nuwamba 1988
  • Burkina Faso 21 Nuwamba 1988
  • Burundi 22 Disamba 1988
  • Cambodia 21 Nuwamba 1988
  • Cape Verde 24 Nuwamba 1988
  • Central African Republic 23 Disamba 1988
  • Chad 01 Disamba 1988
  • Chile 07 Janairu 2011
  • China 20 Nouwamba 1988
  • Colombia 03 Augusta 2018
  • Comoros 21 Nuwamba 1988
  • Congo (Republic of) 05 Disamba 1988
  • Costa Rica 05 Fabrairu 2008
  • Cote d' Ivoire 01 Disamba 2008
  • Cuba 16 Nuwamba 1988
  • Cyprus 18 Nuwamba 1988
  • Czech Republic 18 Nuwamba 1988
  • North Korea 24 Nuwamba 1988
  • Democratic Republic of Congo 18 Disamba 1988
  • Djibouti 17 Nuwamba 1988
  • Dominica 19 Satumba 2011
  • Dominican Republic 15 Yuli 2009
  • Ecuador 27 Disamba 2010
  • Egypt 18 Nuwamba 1988
  • El Salvador 25 Augusta 2011
  • Equatorial Guinea 01 Mayu 1989
  • Eswatini (previously Swaziland) 01 Yuli 1991
  • Ethiopia 04 Fabrairu 1989
  • Gabon 12 Disamba 1988
  • Gambia 18 Nuwamba 1988
  • Georgia 25 Afrilu 1992
  • Ghana 29 Nuwamba 1988
  • Grenada 25 Satumba 2011
  • Guatemala 09 Afrilu 2013
  • Guinea 21 Nuwamba 1988
  • Guinea-Bissau 21 Nuwamba 1988
  • Guyana 13 Janairu 2011
  • Haiti 27 Satumba 2013
  • Honduras 26 Augusta 2011
  • Hungary 23 Nuwamba 1988
  • Iceland 15 Disamba 2011
  • India 18 Nuwamba 1988
  • Indonesia 15 Nuwamba 1988
  • Iran 04 Fabrairu 1988
  • Iraq 15 Nuwamba 1988
  • Ireland 28 Mayu 2024
  • Jamaica 19 Afrilu 2024
  • Jordan 16 Nuwamba 1988
  • Kazakhstan 06 Afrilu 1992
  • Kenya 12 Mayu 1989
  • Kuwait 15 Nuwamba 1988
  • Kyrgyzstan 01 Nuwamba 1995
  • Laos 02 Disamba 1988
  • Lebanon 30 Nuwamba 2008
  • Lesotho 03 Mayu 2011
  • Liberia 19 Yuli 2011
  • Libya 15 Nuwamba 1988
  • Madagascar 16 Nuwamba 1988
  • Malawi 23 Octoba 1998
  • Malaysia 15 Nuwamba 1988
  • Maldives 28 Nuwamba 1988
  • Mali 21 Nuwamba 1988
  • Mauritania 15 Nuwamba 1988
  • Mauritius 17 Nuwamba 1988
  • Mexico 02 Yuni 2023
  • Mongolia 22 Nuwamba 1988
  • Montenegro 24 Yuli 2006
  • Morocco 15 Nuwamba 1988
  • Mozambique 08 Disamba 1988
  • Namibia 19 Nuwamba 1988
  • Nepal 19 Disamba 1988
  • Nicaragua 16 Nuwamba 1988
  • Niger 24 Nuwamba 1988
  • Nigeria 18 Nuwamba 1988
  • Norway 28 Mayu 2024
  • Oman 13 Disamba 1988
  • Pakistan 16 Nuwamba 1988
  • Papua New Guinea 13 Janairu 1995
  • Paraguay 29 Janairu 2011
  • Peru 24 Janairu 2011
  • Philippines 04 Satumba 1989
  • Poland 14 Disamba 1988
  • Qatar 16 Nuwamba 1988
  • Romania 24 Nuwamba 1988
  • Russia 19 Nuwamba 1988
  • Rwanda 02 Janairu 1989
  • Saint Kitts and Nevis 29 Yuli 2019
  • Saint Lucia 14 Satumba 2015
  • Saint Vincent and the Grenadines 29 Augusta 2011
  • Sao Tome and Principe 10 Disamba1988
  • Saudi Arabia 16 Nuwamba 1988
  • Senegal 22 Nuwamba 1988
  • Serbia 16 Nuwamba 1988
  • Seychelles 18 Nuwamba 1988
  • Sierra Leone 03 Disamba 1988
  • Slovakia 18 Nuwamba 1988
  • Somalia 15 Nuwamba 1988
  • Slovenia 04 Yuni 2024
  • South Africa 15 Febrairu 1995
  • South Sudan 14 Yuli 2011
  • Spain 28 Mayu 2024
  • Sri Lanka 18 Nuwamba 1988
  • Sudan 17 Nuwamba 1988
  • Suriname 26 Janairu 2011
  • Sweden 30 Octoba 2014
  • Syria 18 Yuli 2011
  • Tajikistan 02 Afrilu 1994
  • Thailand 18 Janairu 2012
  • The Bahamas 07 Mayu 2024
  • Timor-Leste 01 Maris 2004
  • Togo 29 Nuwamba 1988
  • Trinidad and Tobago 02 Mayu 2024
  • Tunisia 15 Nuwamba 1988
  • Turkey 15 Nuwamba 1988
  • Turkmenistan 17 Afrilu 1992
  • Uganda 03 Disamba 1988
  • Ukraine 19 Nuwamba 1988
  • United Arab Emirates 16 Nuwamba 1988
  • Tanzania 24 Nuwamba 1988
  • Uruguay 16 Maris 2011
  • Uzbekistan 25 Satumba 1994
  • Vanuatu 21 Augusta 1989
  • Venezuela 27 Afrilu 2009
  • Vietnam 19 Nuwamba 1988
  • Yemen 15 Nuwamba 1988
  • Zambia 16 Nuwamba 1988
  • Zimbabwe 29 Nuwamba 1988

Me ya sa sai yanzu Birtaniya za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa?

Gwamnatocin Birtaniya da dama sun taɓa magana kan amincewa da ƙasar Falasɗinu, amma a matsayin wani ɓangare na shirin zaman lafiya tare da kawayenta na yamma.

Amma abubuwan da ke faruwa yanzu da suka haɗa da fama da yunwa a Gaza da fushin da ke ƙaruwa game da hare-haren Isra'ila a Gaza da kuma sauyin ra'ayin jama'a a Birtaniya—duk sun yi tasiri wajen tilasta wa gwamnati ta yanzu ta sauya matsayi.

Sanan kuma ƴan majalisa da ministoci da dama sun matsa wa gwamnati lamba.

A makon da ya gabata a majalisa, an yi ta tambayar dalilin da ya sa Birtaniya ba ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba har yanzu.

Ministan Lafiya Wes Streeting ya ce: ya kamata a yarda da Falasɗinu a matsayin ƙasa "kafin ta lalace gaba ɗaya."

Falasɗinawa ɗauke da buhunan fulawa da aka raba musu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masana lafiya da suka samu goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya sun gargaɗi cewa "mummunan yanayi na yunwa na faruwa a halin yanzu" a Gaza.

Amma Birtaniya ba ta bi sahun Faransa da Ireland da Sifaniya da Norway kawai ba.

Firaminista Keir Starmer ya ɗaura alƙawarin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa da wasu sharudda wanda shi ne ko Isra'ila ta ɗauki matakai na kawo ƙarshen yaƙi a Gaza da kuma dakatar da yunkurin mamaye yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, da kuma shiga shirin zaman lafiya da zai samar da ƙasashe biyu ko kuma ta amince da ƙafa ƙasar Falasɗinu.

Amma gwamnatin Birtaniya ta san babu wani tabbaci cewa Netanyahu zai yarda da wannan shiri cikin makonni shida masu zuwa, domin sau da dama ya ce ba zai amince da kafa ƙasar Falasɗinu ba.

To amma amincewar Birtaniya tana gabatowa. Ko da ashe Netanyahu ya ƙi amincewa da sharuɗɗan da aka ba Isra'ila.

Sai dai kuma Birtaniya ta yau ba kamar ta shekarar 1917 ba ce – ikonta na tasiri ya ragu. Kuma ba a san ko hakan zai kawo sauyi ba.