Ba za mu iya ci gaba da wasa da mutum 10 ba - Arteta

t5

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ƙungiyar "ba za ta juri ci gaba da wasa da mutum 10 ba" bayan jan katin da aka bai wa William Saliba a wasan Bounemouth.

Dan wasan bayan Faransa an bashi kati ne a minti 45 na farkon wasan, wanda daga baya suka yi rashin nasara da ci 2-0, rashin nasara ta farko da suka yi kenan a wannan kakar.

Wannan ne jan kati na uku da aka bai wa ƙungiyar ta Arteta a wannan kakar, bayan wanda aka bai wa Declan Rice a wasan Brigton da na Leandro Trossard a wasan da suka yi canjaras da Man City.

"Wasa da mutum 10 kalubale ne a ko da yaushe," in ji Arteta, wanda aka zirawa kwallo a duka wasanni da aka ba shi jan katin guda uku.

Magana ta gaskiya idan ka yi nazari kansu, za ka ga dalilai uku mabanbanta da kuma sakamako uku, dalilan duka ba su da alaƙa da juna.

"Ba tare da duba hakan ba, gaskiya ba za mu iya ci gaba da wasa da mutum 10 ba, musamman a wannan matakin.

"Akwai buƙatar mu kawar da hakan, a buɗe hakan yake. Dalili ko yaya abin ya faru duk ba ruwanmu da shi. Akwai buƙatar mu ƙara mayar da hankali, hakan kuma yana faruwa a ko ina."

Tun wasan Arteta na farko a Arsenal a ranar 26 ga watan Disamba 2019, an bai wa Gunners jan kati 18, inda ta wuce ko wacce ƙungiya da guda biyar a wannan lokaci.

Saliba ba zai buga wasan da Arsenal za ta yi da Liverpool ba a ranar Lahadi mai zuwa a Premier, amma zai buga mata wasan da za ta yi da Shaktar Donetsk a Champions a ranar Talata.