Man United za ta je Arsenal a FA Cup zagaye na uku

Asalin hoton, Getty Images
Mai rike da FA Cup, Manchester United za ta je Arsenal a karawar zagaye na uku a gasar da za su kece raini cikin watan Janairun 2025 a Emirates.
Ranar Laraba Gunners za ta karɓi bakuncin United a wasan mako na 14 a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
Liverpool kuwa wadda take jan ragamar teburin Premier League za ta fafata da mai buga League Two, Accrington Stanley a Anfield.
A filin wasa na Etihad kuwa za a kece raini tsakanin Manchester City mai rike da Premier League na bara da Salford City.
Tottenham za ta ziyarci Tamworth ɗaya daga ƙungiya biyu da ba sa buga League a Ingila da suka rage a wasannin.
Za a buga wasannin zagaye na uku a FA Cup a karshen mako, wato ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025.
Watakila mai tsaron bayan Everton, Ashley Young mai shekara 39 ya fuskanci ɗansa, Tyler Young, bayan da za a kara tsakanin Everton da Peterborough.
Jadawalin FA Cup karawar zagaye na uku:
- Southampton da Swansea City
- Arsenal da Manchester United
- Exeter City da Oxford United
- Leyton Orient da Derby County
- Reading da Burnley
- Aston Villa da West Ham
- Norwich City da Brighton & Hove Albion
- Manchester City da Salford
- Millwall da Dagenham & Redbridge
- Liverpool da Accrington Stanley
- Bristol City da Wolverhampton Wanderers
- Preston North End da Charlton Athletic
- Chelsea da Morecambe
- Middlesbrough da Blackburn Rovers
- Bournemouth da West Bromwich Albion
- Mansfield Town da Wigan Athletic
- Tamworth da Tottenham
- Hull City da Doncaster Rovers
- Sunderland da Stoke City
- Leicester City da Queens Park Rangers
- Brentford dda Plymouth Argyle
- Coventry City dda Sheffield Wednesday
- Newcastle United da Bromley
- Everton da Peterborough United
- Wycombe Wanderers da Portsmouth
- Birmingham City da Lincoln City
- Leeds United da Harrogate Town
- Nottingham Forest da Luton Town
- Sheffield United da Cardiff City
- Ipswich Town da Bristol Rovers
- Fulham da Watford
- Crystal Palace da Stockport County











