Arsenal na nazarin Sesko da Gyokeres, da wuya Liverpool ta ɗauki Wirtz

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle na son daukar Jamie Gittens a bazara, Wrexham na shirin bai wa dan wasan Fulham Tom Cairney kwantiragin fam 50,000 a mako, Liverpool na tunanin Florian Wirtz zai ci gaba da zama a Jamus.
Newcastle na zawarcin dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jamie Gittens, mai shekara 20, sannan kuma za ta iya daukar abokin wasansa, golan Switzerland Gregor Kobel, mai shekara 27. (Mail)
Dan wasan bayan Fulham Tom Cairney, mai shekara 34, yana jan hankalin Wrexham. Mai shekara 20 din yana taka leda a gasar Championship, inda za a ba tsohon dan wasan na Scotland kwantiragin fam 50,000 duk mako idan ya bar Cottagers a kyauta. (Talksport)
Liverpool na tsammanin Florian Wirtz zai ci gaba da zama a Bayer Leverkusen ko kuma ya koma Bayern Munich amma za su kara tuntubar kungiyarsa don jin ko dan wasan tsakiyar na Jamus mai shekara 22 yana son barin Bundesliga. (Times)
Tsohon dan wasan Ingila Jamie Vardy zai bar Leicester City a wannan bazarar amma dan wasan mai shekaru 38 ba shi da niyyar yin ritaya kuma ya yi imanin zai iya taka leda a gasar Premier. (Sky Sports)
An fara tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya har zuwa 2030 tsakanin Bayern Munich da dan wasanta kuma dan bayan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26 (Sky Germany)
Lazio za ta biya Arsenal kudin da ya kai Yuro miliyan 9 (£7.57m) don daukar dan wasan bayan kasar Portugal Nuno Tavares mai shekara 25 a matsayin aro. (Fabrizio Romano)
Dan wasan Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22, na fuskantar rashin tabbas a nan gaba a Old Trafford inda koci Ruben Amorim ke shirin sayar da wasu 'yan wasa don samun kudin siyan wasu sababbi. (Telegraph)
Bournemouth ta sanya fam miliyan 45 a matsayin farashn dan wasan bayan kasar Hungary Milos Kerkez, mai shekara 21, wanda Liverpool ke nema. (iSport)
Arsenal ta dukufa wajen neman dan wasan gaba, inda take nazarin daukar ko dai dan wasan RB Leipzig Benjamin Sesko na Slovenia, mai shekara 21, ko kuma Viktor Gyokeres dan kasar Sweden mai shekaru 26 na Sporting. (Independent)











