Afcon 2024: Guinea-Bissau ce ta daya a rukunin Super Eagles

Guinea Bissau

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Guinea-Bissau ta dare matakin farko a teburin rukuni na daya a wasannin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a buga a 2024.

Tawagar ta samu wannan damar bayan da ta ci Sao Tome and Principe a wasa na biyar a cikin rukunin ranar Laraba, saura karawa daya ta rage mata.

Ta kuma yi nasarar cin 1-0 ta hannun Zinho Gano a minti na 55 a karawar ta neman shiga wasannin kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a Janairun 2024.

Kawo yanzu Guinea-Bissau ta hada maki 10 a wasa biyar, yayin da Najeriya take da maki tara a wasa hudun da ta buga.

Saliyo kuwa maki biyar ne da ita mai karawa hudu da kuma Sao Tome And Principe mai maki daya, wadda ta yi fafatawa biyar.

Ita dai Guinea-Bissau na fatan samun shiga gasar kofin Afirka karo na hudu a tarihi.

Ranar Lahadi, Super Eagles za ta kara da Saliyo a Liberia, wasa na biyar da kowace cikin kasashen biyu za su buga a cikin rukuni kenan.

Idan Saliyo ta kasa cin Super Eagles ranar Lahadi, kenan Guinea-Bissau da Najeriya sun samu gurbin zuwa Ivory Coast tun kafin a buga karawar karshe ta cikin rukunin.