Smith Rowe zai bar Arsenal, Har yanzu Chelsea na sa ran ɗaukar Osimhen

.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ta shirya barin Antony ya tafi aro, Sergi Roberto yana sha'awar komawa gasar Premier, Crystal Palace ta shirya tayin Emile Smith Rowe.

Crystal Palace ta shirya kai tayin £30m don siyan dan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Emile Smith Rowe, mai shekara 23. (Talksport)

Manchester United na son barin dan wasanta dan Brazil Antony, mai shekara 24, ya tafi aro a wannan bazarar amma idan kungiyar da zai koma ya shirya biyansa albashin fan 70,000 a mako. (ESPN

Dan wasan tsakiya na Spain Sergi Roberto, mai shekara 32, yana kokarin komawa gasar Premier bayan kwantiraginsa da Barcelona ya kare. (Mundo Deportivo)

Chelsea ta yi wa dan wasan tsakiyarta Lesley Ugochukwu mai shekaru 20 kiranye daga tawagar Faransa a gasar Olympics, yayinda rahotanni ke kara karfi cewa tana shirin ba da shi aro a kakar wasa ta bana. (Athletic)

Liverpool ta shirya sayar da golan Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 25, idan ta samu tayin da ya dace. (Fooyball Insider)

Dan wasan Brazil Richarlison, mai shekara 27, a shirye yake ya koma Saudi Pro League amma Tottenham za ta bukaci fan miliyan 60. (HITC)

Leicester ta kai tayin £21m don siyan dan wasan gefe na Juventus Matias Soule, mai shekara 21, kuma tana fatan kulla yarjejeniya da dan wasan na Argentina mako mai zuwa. (Telegraph)

Newcastle na fatan doke West Ham da Juventus wajen siyan dan wasan bayan Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 24, bayan tattaunawa da Nice. (HITC)

Chelsea ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da zawarcin dan wasan Napoli Victor Osimhen, mai shekara 25, duk da cewa Paris St-Germain ce kan gaba wajen zawarcin dan wasan na Najeriya. (CaughtOffside)

Crystal Palace ta fara tattaunawa da Marseille kan yiwuwar sayen dan wasan gefe na Senegal Ismaila Sarr mai shekaru 26. (Athletic)

Chelsea ta samu tuntuɓar Newcastle game da samun ɗan wasan gefe na Ingila Noni Madueke mai shekaru 22. (Footbal Insider)

Liverpool da Newcastle na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan baya na kasar Holland Dean Huijsen, mai shekara 19, amma Juventus kan fam miliyan 25.3 na iya zama cikas. (Tuttosport)

Brighton na neman ci gaba da tattaunawa kan cinikin dan wasan Jamus Brajan Gruda mai shekaru 20 daga Mainz. (Fabrizio Romano)