Ko Man United tana buga kaka mafi muni a tarihi a bana?

Amorim

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta yi ban kwana da FA Cup na bana, sakamakon da Fulham ta doke ta 2-1 a Old Trafford ranar Lahadi.

United ce ke rike da kofin da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, kofin da ya ba ta damar buga Europa League a kakar nan.

Ƙungiyar Old Trafford tana ta 14 a kasan teburin Premier League da maki 33, bayan da ta ci wasa tara da canjaras shida aka doke ta fafatawa 12.

Rabon da ƙungiyar Old Trafford ta yi irin wannan rashin kokarin tun bayan 1974 da ta faɗi daga babbar gasar tamaula ta Ingila.

Kofin Premier League na karshe da United ta ɗauka tun 2012/13, lokacin da Manchester City ta yi ta biyu da tazarar maki 11, kuma na 20 da United ta lashe.

Daga nan Manchester City ta karɓe ragamar lashe babban kofin tamaula na Ingila, Chelsea ta ɗauka sau biyu da Leicester City mai ɗaya, Liverpool ta ɗauka a 2020.

Liverpool na shirin lashe Premier League na bana kuma na 20 jimilla, za ta yi kan-kan-kan da yawan wanda United ta ɗauka a tarihi.

Liverpool ce ta ɗaya a kan teburin Premier na kakar nan da maki 67, sai Arsenal ta biyu mai maki 54.

Real Sociedad za ta karɓi bakuncin United a zagayen ƴan 16 a gasar zakarun Turai ta Europa League ranar Alhamis 6 ga watan Maris.

Wannan kofin shi ne ya rage da United ke fatan ɗauka, wanda zai ba ta damar sake buga wasannin zakarun Turai a badi da zarar ta lashe shi.