Man City ta tattauna da Wirtz, Barcelona da Arsenal na zalama kan Garcia

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta gana da Florian Wirtz, Liverpool kuma ta tuntubi dan wasan gaban Bayer Leverkusen, dan wasan Real Madrid Rodrygo ne ke jan hankalin kungiyoyin Premier League.
Manchester City ta gana da dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz, mai shekara 22, kan yuwuwar siyan Bajamushen a bazara. (Bild)
Sai dai ita ma Liverpool ta tuntubi Wirtz don nuna sha'awar siyan ɗan wasan a wannan bazarar. (Athletic)
Kungiyoyin Premier da suka hada da Manchester City da Arsenal na zawarcin dan wasan gaban Real Madrid Rodrygo, mai shekara 24, yayin da rahotanni ke cewa dan kasar Brazil din yana takun saka da ma'aikatan kulob din. (AS)
Real Madrid na son biyan fam miliyan 50 wajen siyan dan wasan bayan Spain Dean Huijsen, mai shekara 20, daga Bournemouth. (Sky Sports)
Liverpool ba za ta karbi fan 850,000 daga Real Madrid ba domin baiwa dan wasan baya Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, damar komawa kungiyar ta Spaniya da wuri. (Sun)
Newcastle ta kere wa Chelsea a fafatukar sayen dan wasan bayan Ingila Marc Guehi, mai shekara 24, daga Crystal Palace. (Talk)
Bayern Munich ta kulla yarjejeniya da Bayer Leverkusen don siyan dan wasan bayan Jamus Jonathan Tah, mai shekara 29. (Fabrizio Romano)
Barcelona na fafatawa da Arsenal wajen neman golan Espanyol Joan Garcia, mai shekara 24. (AS Spanish)
Barca na son siyan dan wasan baya na tsakiya, da mai tsaron baya da kuma na gefe (ESPN)
Xavi Simons na RB Leipzig a shirye yake ya bar kulob din a bazara, duk da cewa dan wasan tsakiyar Netherlands din mai shekara 22 ya rattaba hannu kan kwantiragi na dindindin a watan Janairu. (Fabrizio Romano)
Bristol City na son ci gaba da rike dan wasan gaba Nahki Wells, mai shekara 34, a kakar wasa mai zuwa, bayan da ya kasa kai wa gasar Premier (Sky Sports)









