City da Barca na gogayya kan Olmo, ƙila Chelsea da Madrid su yi musayar masu tsaron raga

Dani Olmo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Manchester City ta gabatar da buƙatarta ta sayen ɗan wasan tsakiya na RB Leipzig Dani Olmo na Sifaniya mai shekara 26. (Foot Mercato - in French)

Amma kuma Barcelona ma ta gabatar da tayin sayen Olmo a kan fam miliyan 50 (Sky Sports)

Ɗan bayan Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, na shirin kin sabunta kwantiraginsa a Everton har sai ƙungiyar ta yadda ta riƙa biyansa fam160,000 a duk mako kamar yadda Manchester United ta yi masa tayi. (Mail)

Ɗan bayan Manchester United na Ingila Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 26, ya yi watsi ta zawarcinsa da West Ham ke yi kuma zai fi son ya tafi Inter Milan a bazaran nan. (Talksport)

Wataƙila Brentford ta dakatar da shirinta na barin Ivan Toney wanda Tottenham da West Ham ke so, bayan da Igor Thiago da zai maye gurbinsa ya ji rauni a wasannin shirin tunkrar sabuwar kaka. (Sun)

Crystal Palace ta amince da baka ta sayi ɗan wasan gaba na gefe na Senegal, Ismaila Sarr, a yuro miliyan 15 daga Marseille. (Athletic)

Ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Emile Smith Rowe ya kusa kammala komawa Fulham bayan da Mikel Arteta ya ƙi tafiya da shi wasannin sada zumunta na shirin fara gasar bana, da Bournemouth a Amurka. (Guardian), external

Aston Villa na sa ido a kan ɗan wasan gaba na gefe na Borussia Dortmund da Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 22, wanda Juventus da Chelsea ma ke so. (Mail)

Ɗan wasan gaba na gefe na Napoli da Denmark Jesper Lindstrom, mai shekara 24, ya kammala gwajin lafiyarsa a Everton. (Fabrizio Romano)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Watakila mai tsaron ragar Chelsea Kepa Arrizabalaga na Sifaniya ya koma Real Madrid shi ma kuma golan Madrid ɗin Andriy Lunin ya tafi Chelsea. (AS)

West Ham ta gabatar da tayin fam miliyan 30 tare da bayar da ɗan wasanta na tsakiya Lewis Orford na Ingila mai shekara 18, domin sayen ɗan gaban Aston Villa da Colombia Jhon Duran, mai shekara 20. (Athletic )

Nottingham Forest ta ƙi yarda da tayin da West Ham ta yi mata ɗan bayanta na Wales Neco Williams. (HITC)

An gaya wa Liverpool cewa sai ta bayar da fam miliyan 50 idan tana son ɗan bayan Juventus da Brazil Bremer, 27. (Football Insider)

Chelsea ta kusa kammala sayen ɗan bayan Ivory Coast Guela Doue mai shekara 21, daga Rennes a kan fam miliyan 7.6 (Sky Italy)

Haka ita ma ƙungiyar Paris St-Germain na dab da kammala cinikin ɗan wasan tsakiya na Benfica da Portugal Joao Neves mai shekara 19. (Fabrizio Romano)

Tattaunawa ta yi nisa da ɗan wasan gaba na gefe na Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 30, domin barin Newcastle zuwa wata ƙungiya ta Saudiyya wadda ba a ambata ba. (Football Insider)