Derby ta ɗauki Ozoh daga Crystal Palace a matsayin aro

d

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan tsakiya na Crystal Palace David Ozoh ya koma Derby County da taka leda a matsayin aro na tsawon kaka daya.

Dan wasan mai shekara 19 da ya fito daga tawagar yara ta Crystal Palace ya buga wa tawagar manya da take buga Premier 13, sai dai har yanzu bai fara wasa ba ga Eagles.

An haifi Ozoh ne a birnin Valencia da ke Spain, sai dai ya wakilci Ingila a wasannin 'yan kasa da shekara 18, a baya kuma ana ta alakanta shi da komawa Plymouth.

"Ina jin cewa nan tamkar wajen farko ne na gina rayuwar kwallon kafata," kamar yadda Ozoh ya shaida wa shafin kungiyar kwallon kafa ta Derby.

"Na wasu 'yan wasanni a bara a basu da yawa kuma a benci. Kuma hakan ba dadi, Shi yasa na yi tunanin cewa gwara na matsa na samu inda zan riƙa kwallo. Dan haka ina cikin farin ciki sosai a nan."

Hudu cikin 'yan wasa bakwai da Derby ta ɗauka 'yan wasan tsakiya ne, inda Ozoh ya bi bayan Ben Osborn da Kenzo Goudmijn da kuma Ebou Adams.

A ranar Juma'a 9 ga watan Agusta Derby za ta fara kakar bana da Blackburn Rovers.