Rosenior ya maye gurbin Patrick Vieira a matsayin kocin Strasbourg

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Hull City Liam Rosenior ya zama sabon kocin RC Strasbourg bayan korar kocin nan ɗan Faransa.
Dan shekara 40 ɗin shi ne ya kai tawagar Tigers matsayi na bakwai a gasar Championship a bara, amma an a watan Mayu lokacin da Hull City ta kasa kai bantenta a wasan neman gurbi.
Ya maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar Strasbourg a ranar 18 ga watan Yuli kan yarjejeniyar fahimtar juna.
Rosenior ya ce: "na ji dadin komowa cikin fagen fafatawa, kungiyar nan ta Faransa mai dinbin tarihi, magoya baya za su ci gaba da nuna goyon baya da soyayya.
"Zan yi duk abin da zan iya na sanya farin ciki a wannan ƙungiya, ta yi alfahari da 'yan wasanta. Jira nake kawai na fara aikin."
Strasbourg sun kamma gasar bara a matsayi na 13 cikin 20.
Shugaban ƙungiyar Marc Keller ya ce yana farin ciki da zuwa Liam. matashin mai horaswa da zai sauya akalar kungiyar mu.







