Tarihin Sanoussi Tambari Jackou, dan siyasar Nijar da ya shafe sama da shekaru 11 a gidan yari

Asalin hoton, OTHERS
Ranar Litinin 18 ga watan Yulin 2022 ne Allah ya yi wa fitaccen dan siyasar nan na Jamhuriyar Nijar, Sanoussi Tambari Jackou, rasuwa yana da shekara 82 a duniya . Fitaccen ɗan siyasa ne, wanda ya rike muƙamai da dama lokacin da yake raye.
Ya yi gwagwarmaya wajen ci gaban ƙasar a mulkin farar-hula kafin rasuwarsa.
Mutane da dama sun nuna alhinin rasuwarsa, ciki har da shugaban Nijar Bazoum Mohamed, da tsohon shugaban ƙasar Mohammed Issofou.
Tun bayan rasuwar, mutane da dama na ta tambayar shin wane ne marigayin ?
Tarihinsa
An haifi marigayi Sanoussi Tambari Jackou ne a shekarar 1940 a Kornataka, a yankin da yanzu aka sani da Dakoro da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Yana da mata mai suna Françoise, wadda ya haifi ƴaƴa mata biyar da ita, babbar cikinsu ita ce Rakiya Kaffa Jackou, wadda ta taba rike mukamin minista a Nijar.
Mahaifiyarsa ƙabilar Tuareg ce, yayin da mahaifinsa ya kasance Bahaushe, kuma ya fara aiki tun shekarar 1970.
Siyasarsa
Jackou ya dade yana gwagwarmayar siyasa, har ta kai ga an kama shi, bayan rashin nasarar hambarar da gwamnatin Seyni Kountché a watan Maris na shekarar 1976, inda lokacin ne aka tsare shi a gidan yari har sama da shekara goma sha daya bayan mutuwar Kounche.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga baya an sake shi a watan Nuwamban 1987, daga nan ne kuma ya sake komawa aikin gwamnati a 1988.
A farkon 1990, Jackou ya kasance mamba na kafa jam'iyyar Democratic and Social Convention (CDS-Rahama). An zabe shi a Majalisar Dokoki ta kasa a watan Fabrairun 1993 a matsayin dan takarar CDS a mazabar Maradi.
Bayan zaben, ya zama mataimakin shugaban majalisar dokokin Nijar daga 1993 zuwa 1994.
A lokacin mulkin Ibrahim Baré Mainassara, Jackou ya shiga gwamnati a matsayin karamin Ministan Ilimi mai zurfi.
A sakamakon haka, an kore shi daga CDS, inda ya kasance mataimakin shugaba, daga nan sai ya je ya kafa sabuwar jam'iyya, PNA-Aloumat, a farkon 1997, kuma ya ci gaba da kawance a Shugaba Mainassara.
A cikin Afrilu 1998 ya raba gari da Mainassara, wanda daga bisani aka kashe a lokacin juyin mulki shekara guda bayan haka.
Kafin rasuwarsa ya rike mukamin mai ba da shawara ta musamman ga Shugaba Mohamed Bazoum kafin rasuwarsa a birnin Yamai na Jumhuriyar Nijar.
Aikin jarida
Marigayin ya bude wata jaridar mako-mako a Yamai da ake kira La Roue de l'Histoire a ranar 18 ga Mayun 2002.
Amma daga baya an sake kama shi, tare da mawallafin jaridar, saboda kalaman sukar firaminista Hama Amadou, da kuma kalaman da aka yi wa Ministan Kasuwanci Seini Oumarou.
Daga karshe an yanke wa Jackou hukuncin daurin watanni hudu, da tarar CFA 100,000, sannan an tilasta wa jaridar biyan diyya CFA miliyan biyu ga mutanen biyu.
A cikin Disamba 2004, an sake kama Jackou saboda "tayar da kiyayyar kabilanci" a lokacin bayyanarsa a wani shirin rediyo, amma aka sake shi a ranar 9 ga Janairu 2005.
Jackou ya yi aiki a matsayin mai shiga tsakani tsakanin kungiyoyin farar-hula karkashin jagorancin Coalition for Quality and Justice Living.











