Onana ne zai tsare ragar United a wasa da Lyon a Europa League

Asalin hoton, Getty Images
Andre Onana ne zai tsare ragar Manchester United a Europa League da za ta fafata da Lyon ranar Alhamis a Old Trafford, in ji Ruben Amorim.
Ɗan wasan tawagar Kamaru, bai tsare ragar United ba a Premier League da aka doke ta 4-1 a gidan Newcastle ranar Lahadi, wadda ta yi amfani da Altay Bayindir.
A makon jiya United ta tashi 2-2 a gidan Lyon a Faransa a wasan farko zagayen kwata fainal a Europa League.
An kuma ɗora alhakin dukkan ƙwallaye biyun da aka ci United a Faransa a kan sakacin Onana.
Sai dai koci, Amorim ya ce tsohon golan Inter Milan, shi ne zai tsare ragar United a Old Trafford ranar Alhamis.
Bayindir, wanda ya buga gasar Premier League a karon farko, an zarge shi da saka ci a ƙwallo na huɗu da Newcastle ta zura a raga a St James Park.
Amorim ya ce Onana ya cancanci ya koma cikin ƴan wasa 11 da suke fara buga wa United tamaula.
Kociyan ɗan kasar Portugal ya faɗi hakan ne a lokacin da ya gana da ƴan jarida tare da Harry Maguire, wanda ya goyi bayan Onana ya ci gaba da aikinsa.











