Liverpool ta koma ta biyu a Premier League

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool ta koma ta biyun teburin Premier League, bayan da ta ci Fulham 3-1 a Craven Cottage wasan mako na 34.

Liverpool ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Trent Alexander-Arnold a bugun tazara, daga baya Fulham ta farke ta hannun Timothy Castagne.

Daga baya ne Liverpool ta kara na biyu ta hannun Ryan Gravenberch, sannan Diogo Jota ya zura na uku a raga a Craven Cottage.

Kwallo na 100 da Jota ya ci a babbar gasar tamaula ta Ingila a dukkan fafatawa, wanda ya zura 44 lokacin da yake Wolverhampton da kuma 56 a Liverpool.

Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta biyu da maki da maki 74, iri daya da na Arsenal, wadda take kan teburi, sakamakon cin Wolves 2-0 ranar Asabar a Molinuex.

Manchester City, wadda ta kai wasan karshe a FA Cup ranar Asabar, bayan doke Chelsea tana ta ukun teburi da maki 73.

Wannan shi ne wasa na hudu da suka kara a tsakaninsu a bana:

2023/2024

League Cup Laraba 24 ga watan Janairun 2024

  • Fulham 1 - 1 Liverpool

League Cup Laraba 10 ga watan Janairun 2024

  • Liverpool 2 - 1 Fulham

Premier League Lahadi 3 ga watan Disambar 2023

  • Liverpool 4 - 3 Fulham

Liverpool ba ta yi rashin nasara ba a wasa na shida a Premier League a Craven Cottage kenan, wadda ta yi nasara biyar da canjaras daya.

Wasa daya Fulham ta yi nasara a karawa 14 baya da ta fuskanci Liverpool a dukkan fafatawa da canjaras uku da rashin nasara 10.

Liverpool, wadda aka yi waje da ita a Europa League na bana za ta buga wasan Premier League na gaba a gidan Everton ranar Laraba 24 ga watan Afririlu.