Real Madrid ta ci wasa hudu a jere a La Ligar bana

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta doke Real Betis da ci 2-1 a wasan mako na hudu a gasar La Liga da suka kara ranar Asabar a Santiago Bernabeu.

Minti tara da fara wasa Vinicius Junior ya ci wa Real kwallo, sai dai minti takwas tsakani Sergio Canales ya farke wa Betis.

Saura minti 25 a tashi daga wasan Real ta kara na biyu ta hannunRodrygo, wanda ya ssa ta hada maki ukun da take bukata.

Kungiyoyin biyu sun kara a bara, inda Real Madrid ta je ta ci Betis 1-0 ranar 28 ga watan Agustan 2021, sannan suka tashi 0-0 ranar 20 ga watan Mayun 2022 a Santiago Bernabeu.

Tun kan wasan na ranar Asabar Real Madrid ta ci wasa uku da fara kakar nan, inda ta ci Almeria 2-1 a wasan makon farko ranar 14 ga watan Agusta.

Real ta je ta doke Celta Vigo ranar 20 ga watan Agusta, sannan ta yi nasara a gidan Espanyol 3-1 ranar 28 ga watan Agusta.

Itama Betis ta yi nasara a wasa ukun da ta yi, wadda ta fara da doke Elce 3-0 ranar 15 ga watan Agusta.

Sai ta yi ci Mallorca 2-1 ranar 20 ga watan Agusta, sannan ta doke Osasuna 1-0 ranar 26 ga watan Agusta.

Ranar 6 ga watan Satumba Real Madrid za ta ziyarci Celta domin buga wasan farko a cikin rukuni a Champions League na bana.

Real ce ke rike da kofi na 14 jumulla da ta dauka a bara da ta doke Liverpool a wasan karshe a Faransa.

Tuni kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da zai fuskanci Betis.

'Yan wasan Real Madrid:

1. Courtois

2. Carvajal

3. E. Militão

4. Alaba

9. Benzema

10. Modrić

12. Camavinga

18. Tchouameni

20. Vini Jr.

21. Rodrygo

23. F. Mendy.

 

Masu zaman benci:

13. Lunin

26. Luis López

6. Nacho

7. Hazard

8. Kroos

11. Asensio

15. Valverde

17. Lucas V.

19. D. Ceballos

22. Rüdiger

24. Mariano.