Waiwaye: Binciken El-Rufai da musun biyan tallafin man fetur
Wannan maƙala ce da ke kowa muku muhimman batutuwan da suka fi jan hankali a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Majalisar dokokin Kaduna ta buƙaci a bincike gwamnatin El-Rufai

Asalin hoton, KDGOV
A cikin makon da ya gabata ne wani kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin El-Rufai da ta gabata ya miƙa sakamakon bincikensa.
Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i.
Lokacin da ya gabatar da rahoton a ranar Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa'i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba, ko kuma ba a bi ƙa'ida wajen cin bashin ba.
Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne suka zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa'i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi.
Gwamnatin Najeriya ta musanta biyan tallafin man fetur

Asalin hoton, FB/BOLA TINUBU
Cikin makon ne kuma gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba ta sauya matsayarta ba game da cire tallafin man fetur, kamar yadda shugaban ƙasar ya sanar a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Wannan na zuwa ne bayan da wasu kafafen yaɗa labaran ƙasar suka bayyana cewa Najeriya na ci gaba da biyan kuɗin tallafin man fetur ta ƙarƙashin ƙasa.
Inda kafofin suka yi zargin cewa ƙasar ta ware naira tiriliyan 5.4 don biyan tallafin man fetur a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.
To sai dai cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Bayo Onanuga, ta musanta labarain.
“Gwamnati na son jaddada cewa matsayarta kan cire tallafin man fetur ba ta sauya ba daga abin da shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar 29 ga watan Mayu, 2023”
‘Za mu koma yajin aiki bayan mako ɗaya idan...’

Asalin hoton, NLC
An shiga makon da ya gabatan ne da yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya.
To amma a ranar Talata manyan ƙungiyoyin ƙwadago biyu na Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC) suka sanar da dakatar da yajin aikin.
Sai dai sun janye yajin aikin ne bisa wasu sharuɗɗa.
Ƙungiyoyin ƙwadagon sun tsunduma aiki ne bayan gaza cimma matsaya tsakaninsu da gwamnatin tarayya kan abin da zai zama albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata a Najeriya.
Jim kaɗan bayan kammala taron, ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce sun janye yajin aikin ne domin hanzarta tattaunawar da ake yi tsakanin su da gwamnati game da albashi mafi ƙanƙanta, wanda shi ne babban abin da ya janyo taƙaddamar.
Karanta cikakken labarin a nan
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince a ninka albashin alƙalai sau uku

Asalin hoton, Others
A cikin makon ne dai majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wani ƙudirin doka da ke neman ninka albashin Alƙalin Alƙalan ƙasar Olukayode Ariwoola da sauran manyan alƙalan ƙasar sau uku.
Ƙudurin dokar ya tsallake karatu na uku a zaman majalisar na ranar Laraba.
Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin shari'a da 'yancin ɗan'adam da kuma harkokin sharia na majalisar, wanda shugaban sa Mohammed Monguno ya gabatar.
Ɗan majalisar ya ce "biyan wadataccen albashi ga ma'aikatan shari'a zai ba su damar mayar da hankali wajen gudanar da aikinsu ba tare da tunanin wani nauyi na daban ba".
A cewarsa: “Ƙarin albashin zai inganta ƙwarewar aikin ma'aikatan shari'a, lamarin da kuma zai dawo da martabar ɓangaren shari'a a tsakanin jama'ar ƙasa.”
Ƙasa ta rufe mutum 30 a mahaƙar ma'adanai a Neja

Asalin hoton, Getty Images
A farkon makon ne kuma ƙasa ta rufe aƙalla mutum 30 a wata mahaƙar ma'adinai a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro.
Hukumar ta ce an kuma samu nasarar ceto mutum shida da rai, waɗanda suka samu munanan raunuka.
Kan hana ne kuma gwamnatin tarayya ta tilasta wa kamfanonin haƙar ma'adanai yin inshora ga ma'aikatansu, domin bayar kariya gare su idan wani hatsari ya faru.
Yayin da yake jawabi bayan da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ministan ma'adinan ƙasar, Dele Alake, ya ce daga yanzu gwamnati ba za ta sake amincewa da lasisin duk wani kamfanin haƙar ma’adanai da bai nuna ƙwaƙwarar shaidar cika ƙa'idojin gudanar da aiki ba.










