Musulman Indiya da aka zarga da haddasa ambaliyar ruwa

Asalin hoton, EPA
Bayan wata mummunar ambaliya da ta daidaita jihar Assam da ke arewa maso gabashin Indiya, an zargi al’ummomin musulmi a yankin da haddasa ambaliyar.
Amma akwai gaskiya cikin zarge-zargen? Daya daga cikin wadanda aka zarga ya fada wa BBC labarinsa.
Lokacin da ‘yan sanda suka buga kofar dakinsa da safiyar ran 3 ga watan Yuli, Nazir Hussain Laskar ya shiga dimuwa.
A tsawon shekaru, ya kasance ma’aikaci a wani kamfanin gine-gine a jihar Assam, inda yake taimakawa jihar gina wuraren kare kai daga ambaliya.
Sai dai, a safiyar ranar, ‘yan sandan da suka kama mista Laskar sun zarge shi da ‘lalata kayakin al’umma’ – wanda shi kuma ya gina wurin ne domin kare al’ummomi daga barazanar ambaliya.
"Na dauki tsawon shekara 16 ina aiki wa gwamnati domin gina shingayen", a cewar mista Laskar. "Me ya sa zan lalata su?"
Mista Laskar ya dauki kusan shekara 20 a tsare, kafin daga bisani a sake shi kan beli.
Ba a samu hannun sa a zargin da ake yi ba, sai dai na yi ta yayata batun sa a kafofin sada zumunta tun bayan faruwar lamarin.
'Na dauka za a kawo mani hari'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata mummunar ambaliya har sau biyu ta daidaita jihar Assam a watan Mayu da kuma Yuni, inda ta hallaka akalla mutum 192.
Yayin da jihar ke fama da matsalar ambaliya a kowane lokacin damina, a wannan shekara daminar ta sauko da sauri kuma na samu mamakon ruwa da ba a saba gani ba.
Amma galibin masu amfani da kafofin sada zumunta, akwai abin da ke faruwa. Sun yi zargi ba tare da hujja ba cewa mutane ne ke haddasa ambaliyar, kuma sun dora laifin hakan a kan wasu maza na kungiyar musulmi da suka haddasa ambaliyar don daidaita birnin Silchar da ke makwabtaka da su, birni kuma da ‘yan addinin Hindu suka fi rinjaye.
Kama mista Laskar, hada da wasu maza musulmai uku, ya janyo wallafe-wallafe da kuma zazzafar muhawara a kafofin sada zumunta, inda aka zarge su da haddasa ambaliyar domin yakarar wadanda ba musulmai ba.
Mutane da dama sun yi ta yada wallafe-wallafen sau dubbai har da masu fada aji wadanda aka tantance shafukansu.
Wasu kafafen yada labaran cikin gida sun yayata zargin.
Sai dai girman lamarin ya fara damunsa lokacin da yake gidan yari.
Wani gidan talabijin ta ambato sunan mista Laskar, inda take zarginsa da haddasa ambaliya domin yakar wadanda ba musulmai ba.
"Na shiga fargaba da kuma kasa yin barci a daren. Sauran fursunoni na magana kan lamarin. Na dauka za a kawo mani hari.’’
Gaskiyar zargin da ake wa musulmai na haddasa ambaliya domin yakar wasu addinai
Aikin gina shingaye ya faro ne tun shekarun 1950 domin takaita afkuwar ambaliya a jihar Assam.
Jihar na da kilomita 4,000 na shingaye sannan an bayyana cewa yawancinsu ba a gina su da karfi ba kuma za su iya lalacewa.
A ran 23 ga watan Mayu, aka lalata wani shinge da aka gina a kogin Barak, wacce ta bi ta arewa maso gabashin Indiya da kuma gabashin kasar Bangladesh.

Karyewar shingen ya faru ne a lardin Bethukandi inda Musulmi suka fi rinjaye – kuma wannan na cikin dalilai da suka haddasa afkuwar gagarumar ambaliya a birnin Silchar, inda ‘yan Hindu suka fi rinjaye.
"Karyewar da shingen ya yi, na cikin abubuwa da suka sanya faruwar ambaliyar", a cewar Ramandeep Kaur, wani jami’in dan sanda a birnin Silchar.’’
Sai dai ba ta wurin ne kadai ba ruwa ya samu shigowa garin.’’
BBC ta gano cewa wannan lamari ne ya kai ga kama mista Laskar da wasu Musulmai uku. Daga baya, an kama mutum na biyar.
Ba a samu hannun ko daya daga cikinsu ba a zargin lalata shingen.
"Karya wadannan ya faru ne saboda rashin gyara shingayen,’’ a cewar Nirmalya Choudhury, wani farfesa a cibiyar nazarin bala’o’i ta Jamsetji Tata da ke Mumbai.
"Za a iya cewa mutane ne suka haddasu wasu ambaliyar. Za a iya cewa akwai lokuta da dagan-gan mutane suka karya shingayen saboda ruwa ya samu wurin fita, don kar ya janyo ambaliya a yankunansu.’’ a cewar jami’in dan sandan.

Asalin hoton, Reuters
"Babu wani abu mai kama da haddasa ambaliya don ‘yakar wadanda ba musulmi ba’.
A farkon shekarun, hukumomi na samar da wuri a shingayen don ruwa ya wuce. Ba a yi hakan ba a wannan shekara, sannan mutane sun dauki lamarin a kansu.’’
"Domin yin wannan zargi ga musulmi, ya kamata mutum ya bayar da hujjoji,’’a cewar farfesa Choudhury.’’
Wannan matsala ce ta masu ruwa da tsaki, kuma ina ganin ya kamata a samu martani daga manya.’’
'An zarge ni saboda ni Musulmi ne'
A cewar abubuwa da aka fi tattaunawa a kai a shafin matambayi baya bata na Google, batun ‘amfani da ambaliya wajen yakar wadanda ba musulmi ba’ shi aka fi nema a watan Yuli cikin shekara biyar, da kuma ya samu yayatawa a kafofin sada zumunta.
Sai dai, ba yanzu ne karon farko ba da ake lakabawa musulmai zarge-zarge a kafofin sada zumunta a Indiya.
Lokacin annobar korona, akwai wasu lokuta da aka zargi musulmai da yada cutar ta Covid-19 (abin da wasu kafofin yada labarai a Indiya suka kira da amfani da cutar domin yakar wadanda ba musulmai ba).
Masu suka sun ce tarzoma da kalaman kiyayya da kuma labaran karya a kan musulmi sun karu tun 2014, lokacin da jam’iyyar firaminista Narendra Modi Bharatiya Janata ta ‘yan addinin Hindu ta zo kan mulki.
Sai dai jam’iyyar ta musanta hakan.
Sai dai, mista Laskar ya ci gaba da zama cikin fargaba a jihar Assam, tun bayan sako shi a kan sharudan beli.
"Ni da iyalai na na fargabar barin gidan mu. ‘Ya’ya na basa samun damar zuwa makaranta.
Idan zan fita daga gidana, ina saka hular kwano a wasu lokuta domin boye fuskata. Ina fargaba wasu gungu za su farmani.’’
"An zarge ni da ‘haddasa ambaliya don yakar wadanda ba musulmi ba’ saboda ni musulmi ne. Wannan ba gaskiya bane.
Wadanda suke yayata lamarin suna yin abin da bai kamata ba.’’











