William Ruto ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Kenya

.
An wallafa

Hukumar zaben ƙasar Kenya ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Kenya da kashi 50.49 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa.

Hukumar zaɓen ta sanar da sakamakon zaben ne a ranar Litinin da yamma.

An gudanar da zaɓen ne a ranar Talatar da ta wuce 9 ga watan Agustan 2022.

Ratar da ke tsakaninsa da abokin fafatawarsa Raila Odinga ba shi da yawa, inda shi Odingan ya samu kashi 50.4 na yawan uri'un.

An jinkirta sanar da sakamakon saboda zarge-zargen maguɗi da aka dinga yi wa ɓangaren Odinga.

Huɗu daga cikin mambobin hukumar zaɓen bakwai sun ƙi su amince da a fitar da sanarwar sakamakon, suna cewa an yi maguɗi.

.

"Ba za mu yarda da sakamakon zaɓen ba saboda irin maguɗin da aka tafka a zagaye na ƙarshe na zaɓen," in ji Juliana Cherera, mataimakiyar shugaban hukumar zaɓen.

"Za mu bayar da cikakken bayani... sannan muna sake roƙon al'ummar Kenya da su kwantar da hankalinsu. Akwai damar zuwa kotu kuma shari'ar za ta yi abin da ya dace," in ji ta.

Wannan ne karo na farko da Mista Ruto mai shekara 55 ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Kafin yanzu ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa har tsawon shekara 10, amma sai ya ɓata da Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda ya nuna goyon bayansa ga Odinga.

Jawabin sabon zaɓaɓɓen shugaban Kenya

A yayin da yake jawabi bayan sanar da nasararsa, William Ruto ya ce "Yammaci ne mai matuƙar daɗi... dukkan iko ya tabba ga al'ummar Kenya.

"Ina so ni gode wa Ubangiji da ya kawo mu wannan gaɓa.

"Na san an yi hasashen cewa ba zan kai labari ba - amma da yake abin na Ubangiji ne, ga shi nan na samu.

"Ina miƙa godiyata ga ɗaukacin al'ummar Kenya."

Yadda sakamakon yake

Ga dai yadda bayanin sakamakon zaɓen yake:

An sanar da William Ruto a amtsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Kenya da kashi 50.49 na yawan ƙuri'un.

Sai Raila Odinga ya samu kashi 48.8.

Su kuwa ƴan takara George Wajackoyah da David Mwaure jumullar ƙuri'un da suka samu bai kai kashi ɗaya cikin 100 na ywan ƙuri'un ba.