Ƙayattatun hotunan Mauludi a faɗin duniya

An wallafa

Wasu daga cikin al'ummar Musulmai sun yi imanin cewa an haifi Annabi Muhammadu (SAW) a ranar 12 ga watan Rabiul Awwal na shekarar Hijira.

Hakan ta sa miliyoyin Musulman kan yi bikin tunawa da ranar a kowace shekara, wadda ta wannan shekarar ta yi daidai da 8 ga watan Oktoba.

Mun duba wasu ƙayatattun hotunan yadda bikin ya gudana a wasu ƙasashe na duniya.