Liverpool ta taka rawar gani a bana - Alexander-Arnold

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron baya, Trent Alexander-Arnold ya ce Liverpool ta taka rawar gani a kakar nan, duk da ƙalubalen da ta ci karo da shi a bana.
Bayan da ƙungiyar ta lashe Carabao Cup cikin watan Fabariru, tana cikin takarar daukar kofi hudu jimilla a kakar.
To sai dai ƙungiyar ta ci karo da koma baya, wadda Manchester United ta fitar da ita a FA Cup, sannan Atalanta ta yi waje da Liverpool a Europa League cikin Afirilu.
Haka kuma Liverpool ta rasa kofin Premier League a bana, bayan da Crystal Palace ta yi nasara a kan ƙungiyar Anfield.
Liverpool ta sa ran lashe kofuna da yawa domin taya Jurgen Kloop murna, wanda ya ajiye aiki bayan karshen kakar nan, wanda ya yi kaka tara a Anfield.
Sai dai Liverpool, wadda ta buga Europa League a kakar nan za ta buga Champions League a badi, bayan da ta yi ta uku a teburin Premier League a kakar nan.
Shi kansa Alexander-Arnold, wanda ake sa ran yana cikin wadanda za su buga wa Ingila Euro 2024 ya yi jinyar wata biyu.
Tuni Liverpool ta dauki Arne Slot a matakin wanda ya maye gurbin Kloop daga Feyenoord ta Netherlands.
Sabon kociyan zai fara aiki daga ranar Asabar, zai kuma je Anfield tare da Sipke Hulshoff, wanda shi ne mataimakinsa a Feyenoord.











