City ta kai wasan karshe a FA Cup za ta kara da Crystal Palace

Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta kai wasan karshe a FA Cup na kakar bana, bayan da ta doke Nottingham Forest 2-0 ranar Lahadi a Wembley.

Minti biyu da take leda City ta fara zura ƙwallo a ragar Forest ta hannun Rico Lewis, kuma haka suka je hutu ƙungiyar Etihad na cin 1-0.

Lewis mai shekara 20 da kwana 157 ya zama matashin City da ya ci ƙwallo a Wembley, bayan Steve MacKenzie a Mayun 1981 mai shekara 19 da kwana 172 a FA Cup da Tottenham.

Bayan da suka yi hutu ne suka koma zagaye na biyu City ta kara na biyu ta hannun Josko Gvardiol.

Da wannan sakamakon City za ta kara da Crystal Palace a wasan karshe a FA Cup a Wembley ranar 17 ga watan Mayu a Wembley.

Palace ta kawo wannan gurbin, sakamakon yin nasara a kan Aston Villa da cin 3-0 a Webley ranar Asabar.

Ƙungiyar Etihad tana da FA Cup bakwai a tarihi, ita kuwa Palace na fatan lashe na farko a tarihi.

Arsenal ce kan gaba a yawan Lashe FA Cup a tarihi mai 14, sai Manchester United mai 13 da kuma Chelsea da Liverpool da Tottenham da kowacce take da takwas.

City, wadda take ta huɗun teburi a Premier da tazarar maki ɗaya tsakani da Newcastle, za ta fafata da Wolves ranar Juma'a a Etihad.

Daga nan ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama za ta je Southampton ranar Asabar 10 ga watan Mayu, domin buga Premier League a St Mary.

Tun a ranar Asabar aka tabbatar da ukun da za su koma Championship a baɗi da ya hada da Ipswich Town da Leicester City da kuma Southampton.

Saura wasa huɗu-huɗu ya rage a kammala kakar tamaula ta kakar nan ta Premier League.