Newcastle ta sake taya Guehi na Crystal Palace karo na uku

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United ta kara taya Marc Guehi na Crystal Palace karo na uku, inda BBC ta fahimci cewar ta taya shi kan £60m.
Ƙudin ya kai £55m da za ta fara biya da karin tsarabe-tsaraben da zai kai £5m.
To sai dai Palace ta ce darajar mai tsaron bayan tawagar Ingila ta kai £70m, musamman saboda rawar da mai shekara 24 ya taka a Euro 2024.
Tayi na biyu da Newcastle ta yi wa ɗan ƙwallon ya kai £50m.
Saura yarjejeniyar kaka biyu da ta rage wa Guehi a Palace, wadda take fatan ta sayar da shi ga tsoka.
Ƙungiyoyi da yawa na bibiyar mai tsaron bayan, wanda ya koma Selhurst Park da taka leda daga Chelsea - ya buga wa Palace wasa 111.
Haka kuma Palace na duba yadda za ta yi ta sake ɗaukar Wilfried Zaha, domin ya buga mata wasannin aro a kakar nan.
Mai shekara 31 ya bar ƙungiyar a karshen kakar 2022-23 zuwa Galatasaray, wanda ke ƙwadayin buga Champions League kafin ya yi ritaya.
Zaha ya ci ƙwallo 10 a wasa 42 a ƙungiyar Turkiya har da cin Manchester United a Champions League da suka yi nasara 3-2 a karawar cikin rukuni.
Ɗan wasan tawagar Ivory Coast ya yi karawa 458 a Palace a kaka biyu da cin ƙwallo 90 kuma 68 a Premier League ya zura a raga.










