Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Real da aka gayyata tawagoginsu domin buga tamaula
Ƴan wasan Real Madrid takwas ne aka gayyata, domin buga wa tawagoginsu wasanni tun daga makon nan.
Cikinsu sun haɗa da Bellingham da Rudiger da Camavinga da Modric da kuma Arda Guler.
Sauran sun haɗa da Vini Jr da Valverde da kuma Brahim, domin buga Nations League da wasannin neman shiga gasar kofin duniya da ta Afirka.
Ingila
- Girka da Ingila (Alhamis, 14 ga watan Nuwamba)
- Ingila da Ireland (Lahadi, 17 ga watan Nuwamba)
Bellingham zai buga wa Ingila Nations League da za ta kara da Girka da kuma Ireland.
Faransa
- Faransa da Israel (Alhamis, 14 ga watan Nuwamba)
- Italiya da France (Lahadi, 17 ga watan Nuwamba)
Camavinga zai yi wa Faransa karawar da za ta yi da Israela da Italiya a Nations League.
Brazil
- Venezuela da Brazil (Alhamis, 14 ga watan Nuwamba)
- Brazil da Uruguay (Laraba, 20 ga watan Nuwamba)
Brazil ta gayyace Vini Jr domin buga mata wasan neman shiga gasar kofin duniya a 2026 zai kuma fuskanci Valverde na Uruguay.
Croatia
- Scotland da Croatia (Juma'a, 15 ga watan Nuwamba)
- Croatia da Portugal (Litinin, 18 ga watan Nuwamba)
Ƙyaftin din Real Madrid da Croatia, zai ja ragamar wasan da tawagar za ta yi da Scotland da kuma Portugal.
Morocco
- Gabon da Morocco (Juma'a, 15 ga watan Nuwamba)
- Morocco da Lesotho (Litinin, 18 ga watan Nuwamba)
Brahim zai buga wa Morocco wasan neman shiga gasar kofin Afirka da za ta yi da Gabon da kuma Lesotho.
Jamus
- Jamus da Bosnia and Herzegovina (Asabar, 16 ga watan Nuwamba)
- Hungary da Jamus (Talata, 19 ga watan Nuwamba)
Rudiger yana cikin waɗanda Jamus ta gayyata, domin buga mata Nations League da za ta yi da Bosnia da kuma Hungary.
Turkiya
- Turkiya da Wales (Asabar, 16 ga watan Nuwamba)
- Montenegro da Turkiya (Talata, 19 ga watan Nuwamba)
Arda Guler zai yi wa Turkiya wasan Nations League da za ta fafata da Wales da kuma Montenegro.
Uruguay
- Uruguay da Colombia (Asabar, 16 ga watan Nuwamba)
- Brazil da Uruguay (Laraba, 20 ga watan Nuwamba)
Valverde zai yi wa Uruguay wasan neman shiga gasar kofin duniya da za ta kara da Colombia da kuma Brazil, inda zai fuskanci Vini Jr.