Ramsey na son zama kocin Wales a nan gaba

Asalin hoton, Getty Images
Aaron Ramsey ya bayyana burinsa na zama kocin Wales a nan gaba.
Ramsey mai shekara 33, ya samu lasisin Uefa na zama koci, kuma yanzu haka yana matsayin koci kuma ɗan wasa a Cardiff City.
Kyaftin ɗin Wales ɗin na da goyon bayan kocin ƙasar na yanzu Craig Bellamy, wanda yace yana da kwarin gwiwar idan Ramsey ya zama koci zai kai babban matsayi.
Saboda bibiyar Bellamy sau da ƙafa a aikin da yake yi a matsayin kocin Wales, Ramsey ya tabbatar da cewa zai zama koci a nan gaba.
"Yan shekaru ne kaɗan nan gaba, amma babu shakka abu ne da zai zama muradina watarana," in ji tsohon ɗan wasan Arsenal da Jeventus ɗin ya bayyanawa Sky Sports.
"Lokacin zai zama na alfahari a gare ni ko shakka babu.
"Na samu lasisina, kuma kwanan nan matsayinsa zai ƙaru, abu ne da zai ƙayatar da ni nan gaba."
Ramsey - yana fama da jinya - yana zaune a benci lokacin da Cardiff City ta lallasa Olymouth Argyle a makon jiya kuma ya shika bayar da na shi shawarwarin ga kocin riƙon kwarya Omer Riza.
"Ina ɗan zuwa cikin tawagar Cardiff ta 'yan ƙasa da shekara 18, kuma ina ɗan koyar da su," in ji Ramsey.
"Abu ne da yake zama jiki, kuma ka riƙa kallon wasanni daban-daban."
Tun lokacin da ya ji rauni a cinyarsa a wasan da Wale suka ci Montenegro a watan Satumba, Ramsey bai bugawa Wales wasa ba.
Ya koma atisaye amma bai iya buga wasan da suka yi na biyu ba a wannan watan, yanzu kuma ba a sani ba ko zai gama warkewa gabanin wasanni biyun ƙarshe na Wales da za ta yi da Turkiyya da kuma Iceland a watan gobe a Nations Lig.
Wales ba ta yi rashin nasara ba a wasanni huɗu da ta buga ƙarƙashin Bellamy, kuma Ramsey na gamsuwa da ayyukan kocin.
"Ya zu a lokacin da ake buƙata, shi da tawagarsa na taka rawar da ta kamata," in ji shi.











