Man City ta cimma yarjejeniyar baka da baka kan ɗaukar Marmoush

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta kusan ɗaukar ɗan wasan Eintracht Frankfurt, Omar Marmoush.
Wata majiya ta sanar da BBC cewar an cimma yarjejeniya ta baka da baka tsakanin ƙungiyoyin, amma ba a kammala cinikin ɗan ƙwallon ba.
Ɗan wasan tawagar Masar, mai shekara 25 ya ci ƙwallo 15 a Bundesliga a kakar nan.
Marmoush ya koma taka leda a Eintracht daga Wolfsburg a 2023, bayan da ƙwantiraginsa ya kare da ƙungiyar da ke buga Bundesliga.
Ana sa ran City ta kusan kammala sayen ɗan ƙwallon Brazil, Vitor Reis daga Palmeiras, wanda zai je a auna koshin lafiyarsa.
Haka kuma ƙungiyar Etihad na son sayen ɗan wasan Juventus mai tsaron baya, Andrea Cambiaso, sai dai wasu rahotannin na cewar ba a tattauna ba kan cinikin ɗan wasan tsakaninsu.
Cambiaso, mai shekara 24, ya koma Juventus daga Genoa a 2022, wanda ya ci ƙwallo biyu ya bayar da biyu aka zura a raga a karawa 25 a bana.
Har yanzu City ba ta sanar da kammala cinikin ɗan wasan tawagar Uzbekistan mai tsaron baya Abdukodir Khusanov ba, bayan sanar da ƙulla yarjejeniyar £33.6m da Lens.











