Waiwaye: Komawar gwamnan Delta APC da ɓullar sabuwar ƙungiyar ƴanbindiga
Wannan maƙale ce da ke kawo muku bitar muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin mako mai ƙarewa.
Gwamnan Delta Oborevwori ya koma APC

Asalin hoton, X/Oborevwori
A tsakiyar makon ne dai gwamnan jihar Delta da ke yankin Neja Delta a kudancin Najeriya, Sheriff Oborevwori ya fice daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jami'yyar APC mai mulki a ƙasar.
Wani hadimin gwamnan ne ya tabbatar wa da BBC hakan a wata da tattaunawa ta wayar tarho.
Oborevwori ya fice ne bayan wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ta gudana a fadar gwamnatin jihar da ke Asaba.
Gwamnan wanda ya ci zaɓe a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP ya samu tarba daga wajen manyan ƴansiyasa na jam'iyyar APC a wani mataki da ake kallo na da nasaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da ke tafe.
Sabuwar ƙungiyar ƴan bindiga ta ɓulla a jihar Kwara

Asalin hoton, Getty Images
Haka a makon da muke bankwan da shi ɗin ne aka samu labarin ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ake kira 'Mahmuda' a jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya.
Ƙungiyar ta zafafa ayyukanta na addabar jama'a a wasu garuruwa na ƙananan hukumomin Kaiama da Baruten na jihar.
Bayanai sun ce ƴan ƙungiyar sun samu mafaka ne a gandun dajin Kainji Lake National Park, kuma daga can ne suke kai hare-hare a garuruwan da ke makwabtaka da dajin har ma da wasu sassa na jihar Neja mai maƙwabtaka.
Yanzu haka dai mutanen garuruwan da abin ya shafa na ta yin hijira zuwa wasu wurare, domin guje wa hare-haren ƙungiyar ta Mahmuda.
Mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa dama ƙungiyar ta taɓa kafa sansani a ƙananan hukumomin Kaiama da Baruten.
Tinubu ya umarci hafsoshin tsaro su kawo ƙarshen rikicin Plateau da Borno

Asalin hoton, Bayo Onanuga
A cikin mako ne kuma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro da take ƙara ƙamari a jihohin Borno da Filato da Binuwai da kuma Kwara.
Wannan na zuwa ne bayan ganawarsa da shugabannin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja, inda suka yi nazari a kan yanayin tsaro a Najeriya.
A wata sanarwa da ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyan, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana damuwa kan kisan ƴan Najeriya da ba su ji ba, ba su gani ba a sassan ƙasar.
Shugaban ƙasar, wanda ya shafe fiye da sa'oi biyu yana ganawa da shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, ya ce dole ne su kawo ƙarshen kisan mutane a ƙasar.
Kawu Sumaila ya koma APC bayan ficewa daga NNPP

Bayan jan ƙafa na tsawon lokaci, a cikin makon nan ne ɗaya daga cikin ƴan majalisar dattawa na jam'iyyar NNPP Sanata Abdurahman Kawu Sumaila daga jihar Kano, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Matakin na zuwa ne bayan shafe watanni ana takun saƙa tsakanin Sanatan da jam'iyyarsa ta NNPP a jihar Kano.
A makon da ya gabata ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci wata tawagar yanmajalisar tarayya na NNPP inda suka gana da shugaban jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Kano.
A hirar da ya yi da BBC, Sanatan ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar NNPP, inda ya tabbatar da cewa ya ɗauki matakin ne domin samar da ci gaba ga al'ummar mazaɓarsa.
Gwamnatin Najeriya za ta bai wa maniyyata kuɗin guzirinsu a hannu

Asalin hoton, Getty Images
Haka ma a farkon makon ne gwamnatin Najeriya ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.
Wata sanarwa daga ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ta ce shi ne ya nema wa mahajjatan sauƙin daga Babban Bankin Najeriya CBN.
"An bayyana damuwa game da tsarin da CBN ya sharɗanta na kowane mahajjaci ya yi amfani da katin banki a matsayin wanda zai iya kawo tarnaƙi ga tsari da aikin gudanar da Hajjin 2025," in ji sanarwar da Stanley Nkwocha ya fitar.
Ta ambato kwamashinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na hukumar alhazai, Aliu Abdulrazaq, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.
Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai

Asalin hoton, Getty Images
Daga ƙarshe kuma a cikin makon ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta sake ɗaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu.
Ƙaramin Ministan ma'aikatar jin-ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami'an gwamnati a Abuja.
Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki.
Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasar baki ɗaya.











