Chelsea ta ɗauki aron Sancho daga Man United

Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta kammala ɗaukar aron ɗan wasan Manchester United, Jadon Sancho zuwa karshen kakar bana.

Cikin ƙunshin yarjejeniyar, Chelsea za ta iya sayen Sancho mai shekara 24 kan £20 zuwa 25m a baɗi idan ya taka rawar gani.

Sancho ya koma United kan £73m daga Borussia Dortmund a Yulin 2021, amma sai ya ci karo da koma baya a Old Trafford.

Ya buga karawa 83 a kaka uku a United, daga baya ya samu saɓani da Erik Ten Hag, wanda ya bukaci ɗan wasan tawagar Ingila ya koma yin atisaye shi kaɗai.

Ɗan wasan ya je aro a Dortmund daga Janairu, inda ƙungiyar Jamus ta kai wasan karshe a Champions League, wanda Real Madrid ta lashe kofin a Wembley.

Sancho ya koma United kan fara kakar nan, amma bai buga wasa biyu na Premier League ba da ta fara a kakar nan.

Rabon da ya buga wa tawagar Ingila tamaula tun 2021, wanda ba a gayyata gasar cin kofin duniya a Qatar a 2022 ba da Euro 2024.