Dembele ya ci ƙwallo karo na 10 a jere bayan da PSG ta doke Brest

Asalin hoton, Getty Images
Ousmane Dembele ya ci gaba da sa ƙwazo a cin ƙwallaye, bayan da Paris St-Germain ta je ta doke Brest 3-0 a wasan cike gurbi a Champions League ranar Talata.
Dembele ya zura biyu a raga karo na 10 yana cin ƙwallaye a jere a PSG, kuma na 18 jimilla a wasa 11 baya a dukkan fafatawa.
Ɗan wasan tawagar Faransa ya ci uku rigis a gasar zakarun Turai da Stuttgart.
Wasu ƴan wasa kaɗan ne da suka zura ƙwallo uku rigis a wasa biyu a jere a Champions League da ya haɗa da Lionel Messi a Barcelona a 2016 da Cristiano Ronaldo a Real Madrid a 2017.
Dembele bai samu kafa wannan tarihin ba, wanda aka sauya shi da Goncalo Ramos a minti na 82 a fafatawar.
Kenan Dembele ya ci ƙwallo 14 a Ligue 1 da Champions League a 2025.
Tun kafin Dembele ya zura biyu a ragar Brest, Vitinha ne ya fara ci a bugun fenariti a minti na 21 da fara tamaula, wanda ke wasan aro daga Wolves.
Wannan shi ne wasan farko zagayen cike gurbi a sabon fasalin Champions League, za su kara a wasa na biyu a Paris ranar 19 ga watan Fabrairu.
PSG, wadda ba ta taɓa ɗaukar Champions League ba, an kusan fitar da ita a gasar bana a cikin rukuni, daga baya ta kara ƙwazo da ta doke Manchester City da Stuttgart a wasanninta na gaba.
Ana sa ran PSG za ta kai zagayen gaba cikin ruwan sanyi, wadda ake sa ran watakila ta fuskanci Liverpool ko kuma Barcelona a zagayen ƴan 16.











