Ina ya kamata Liverpool ta ƙarfafa a watan Janairu?

Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A tsawon shekarar 2024, an zura wa Liverpool ƙwallo 42 - hakan na nufin an zura mata 17 fiye da Arsenal ta biyu a kan tebur a shekarar.

Ƙungiyar ba ta saba barin ƙwallaye da yawa na shiga ragarta ba, yayin da tsaron bayan ƙungiyar ke ci gaba da ƙarfafa a ƙarƙashin sabon koci Arne Slot.

Ƙungiyar kan fuskanci jinyar 'yan wasan baya a wasu lokuta cikin kakar da muke ciki, kuma har yanzu akwai ƙalubale a tsaron bayan ƙungiyar.

Yayin da ake cewa, Joe Gomez ya samu rauni a wasan da ƙungiyar ta doke West Ham da ci 5-0, sannan kuma dama Ibrahima Konate na jinya, hakan na nufin ƙungiyar na da 'yan wasan baya biyu kawai masu lafiya, Virgil van Dijk da Jarell Quansah.

Ana sa ran dawowar Konate a farkon shekarar da muka shiga, amma jajircewarsa ka iya zama maras tabbas, don haka idan har wani abu ya samu Van Dijk, to dole ƙungiyar ta fuskanci ɓaraka.

Idan har Liverpool na son ƙarfafa kanta a wannan wata, ɗan wasan baya ne zai zamo babban abin da za ta fi mayar da hankali a kai.

Wane hali ake ciki game da Alexander-Arnold?

Trent Alexander-Arnold.

Asalin hoton, Getty Images

An ci gaba da alaƙanta Real Madrid da ɗan wasan bayan na Liverpool da Ingila.

Liverpool ta yi watsi da tayin Madrid a wannan watan, amma rahotonni na cewa ƙungiyar da ke Sifaniya na ci gaba da matsala lamba domin ɗaukar ɗan wasan.

A yayin da ya rage wata shida kwantiraginsa ta ƙare da Liverpool, Alexander-Arnold na da damar ƙulla yarjejeniya da wasu ƙungiyoyin a nahiyar Turai.