Mahukuntan Man United na goyon bayan Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images
Mahukuntan Manchester United na goyon bayan Erik ten Hag, duk da koma baya da ƙungiyar ke fuskanta da fara kakar bana.
Kociyan ɗan kasar Netherlands na fuskantar kalubale da fara kakar nan tun bayan da Liverpool ta doke United 3-0 ranar Lahadi a Old Trafford a Premier League.
United ta fara da cin Fulham a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila a gida, sannan ta yi rashin nasara a gidan Brighton a wasan mako na biyu.
Hakan ya sa United ta yi kasa zuwa mataki na 14 a kasan teburin Premier League da maki uku a wasa uku.
A bara United ta kare a mataki na takwas a teburin gasar - rashin kokari mafi muni a ƙungiyar tun bayan 1990, sai dai ta lashe FA Cup.
Ta yi nasarar ɗaukar FA Cup, bayan doke Manchester City a Wembley, wanda hakan ya ba ta damar shiga Europa League a kakar nan.
Wasan da United za ta kara a mako na huɗu shi ne da Southampton ranar 14 ga watan Satumba, idan ta yi rashin nasara zai zama ƙwazo mafi muni tun 1986-87, lokacin da ta haɗa maki ɗaya a wasa huɗu.
Hakan ya sa a cikin wata biyu aka kori koci, Ron Atkinson aka maye gurbinsa da Sir Alex Ferguson.
To sai dai mahukuntan United na goyon bayan Ten Hag kan aikin da yake gudanarwa a kaka ta ukun da yake jan ragamar ƙungiyar.
Kafin wasan da Liverpool ta doke United, babban jami'i, Omar Berrada da daraktan wasanni, Dan Ashworth sun ce tun kafin su kara ƙulla yarjejeniya da Ten Hag sai da suka auna ƙwazonsa, sannan suka yanke shawarar ci gaba da aiki da shi.
''Muna goyon bayan Erik. Muna da ya kinin zai mayar da ƙungiyar kan ganiya.
''Mun yi aiki tare da shi wajen sayo ƴan wasa kan fara kakar nan, kuma za mu ci gaba da yin haka, domin samun sakamakon da zai mayar da ƙungiyar kan turba.''











