Zakarun Turai: 'Newcastle za ta iya ba Barcelona mamaki'

Karawar Newcastle da Barcelona

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, A karawarsu ta farko a 1997 Faustino Asprilla ya zura kwallo uku a ragar Barcelona
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon danbayan Newcastle United John Anderson yana ganin damar shigar gasar Turai da kungiyar ta yi a baya-bayan nan za ta iya sa su samu nasara a wasansu na farko da za su yi na gasar ta bana ranar Alhamis din nan a filinsu St James' Park da Barcelona.

A hirarsa da BBC Anderson ya ce : ''Kasancewar yawancin 'yan wasan sun taba taka leda a gasar ta Zakarun Turai a baya lalle wannan zai iya ba su nasara.''

"Ba wai kamar a ce za su shiga gasar ba ne ba su san abin da ake tsammani daga gare su ba ne - yawancinsu sun san gasar sun taka rawa a wasanninta kuma sun san abin da ake sa rai daga wajensu,'' in ji shi.

Ya kara da cewa: "Tuni sun yi babban gumurzu da Paris St-Germain a filinsu na St James' Park - inda suka yi nasara 4-1, wanda wannan babban abin karfafa gwiwa ne. Muna fatan abin da za mu sake gani kenan a karawarsu da Barcelona, wadda tana daya daga cikin manyan kungiyoyin Turai.

"Idan aka kwatanta yadda kungiyar take a baya lokacin da ta kasance a gasar ta Zakarun Turai a karshe, yanzu tawagar ta kara karfi sosai akwai kuma tarin 'yanwasa da Eddie Howe zai zaba ya darje.

"Nasarar da ta samu ta 1-0 a kan Wolves ita ma ta zo a daidai lokacin da za ta ba kungiyar ta Newcastle kwarin gwiwa." A cewar Anderson.

Wannan shi ne karo na biyar da kungiyoyin biyu za su hadu a wasannin gasa, inda Newcastle ta yi nasara da ci 3-2 a karawarsu ta farko a watan Satumba na 1997, a lokacin da Faustino Asprilla ya ci kwallo uku gaba daya.

To amma kuma Newcastle din ta yi rashin nasara a sauran wasanninsu uku na gaba, to amma magoya bayanta suna da kwarin gwiwa a wannan karon.