Zaben shugaban Amurka: Manyan fata biyu kan zaben

Mataimakiyar shugaban Amurka kuma ƴar takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Democrat Kamala Harris da tsohon shugaban Amurka kuma ɗan takara na jam'iyyar Republican Donald Trump

Asalin hoton, X/Multiple

Bayanan hoto, Mataimakiyar shugaban Amurka kuma ƴar takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Democrat Kamala Harris da tsohon shugaban Amurka kuma ɗan takara na jam'iyyar Republican Donald Trump
    • Marubuci, Haruna Ibrahim Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da lokacin zaben shugaban kasar Amurka ke karatowa, har yanzu 'yan kasa ba su manta da abin da ya faru ranar 6 ga watan Junairun 2021 ba.

Harin da aka kai ginin majalisar dokokin kasar na Capitol, na ci gaba da girgiza Amurkawa da duniya baki daya.

Hakan ya janyo zazzafar muhawara, da darsa shakkun anya kuwa dimukradiyya ba ta cikin barazana.

Magoya bayan Shugaba Donald Trump da ba su yi farin ciki da sakamakon zaben 2020 ba, sun yi kokarin hana 'yan majalisa kirga kuri'u na musamman (Electoral College) domin kammala ayyana nasarar Shugaba Joe Biden a matsayin zababben shugaban Amurka.

Wani bincike da kwamitin da majalisar wakilan ƙasar ta kafa ay yi, ya ce harin na Capitol daya ne daga cikin shirin da Trump ya yi na juya sakamakon zaben.

Shekaru hudu bayan nan, Amurkawa za su sake fita domin kada kuri'ar sabon shugaban kasa. Shugaba Biden da ke kan mulki ya janye daga takarar neman wa'adin mulki na biyu, wanda ya share wa mataimakiyarsa Kamala Harris hanyar zama 'yar takarar Democrat.

A wannan karon, za su fafata ne da Donald Trump na Republican a zaben da ake ganin zai yi zafi da daukar hankali a Amurka da duniya baki daya.

Tun a shekarar 1890, zaben shugaban Amurka ke jan hanklain duniya, amma zaben da za a yi na wannan shekara ta 2024 ya sha banbanta da na baya, saboda shi ne na farko tun bayan harin da aka kai Capitol a shekarar 2021.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sakataren harkokin cikin gida Steve Simon ya shaida wa shirin horas da kwararrun 'yan jarida a Minnesota cewa, yana da buruka ko fata biyu kan zaben na 2024; wato mutane za su fito kwansu da kwarkwata, sannan za a samu saukin hargagi.

Simon ya ce idan aka dauki fannin fitowa kada ƙuri'a, yana da kwarin gwiwar jama'ar Minnesota za su ci gaba da zama ja-gaba na wadanda suka fi kowa fitowa zaben kamar yadda aka saba bisa al'ada, da lokutan zaben baya.

“Wannan ce jihar Minnesota, ina da kwarin gwiwa a nan,” in ji shi. “Ina da kyakkyawan fata mu za mu kasance sahun gaba, yadda dai muka saba, kai ko ba mu kasance na farko ba, tabbas za mu zama a sahun gaba a jihohin Amurka.”

Dama dai jihar ta Minnesota, na da dadadden tarhin ruwan kuri'u a duk lokacin zabe, ko a shekarar 2020 sama da kashi 79 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri'a su ne suka fito zaben, hakan ya sanya ta zama ta daya a daukacin Amirka.

Ana sa ran fitowar masu zabe a wannan karon zai yi tasiri, kamar yadda aka gani a baya. Idan an fito hakan na nufin nasara, amma idan ba a fito ba hakan na nufin masu kada kuri'a su na adawa da zaben.

Simon ya ce; “Idan ina magana akan danbarwa, ba ina nufin babu mai fitowa zabe ko rashin karsashin fitowar ba, abin da na ke nufi shi ne, dole abi doka da oda a wannan karon. Dole mu rungumi sakamakon zaben yadda ya zo, ko da bai mana dadi ba. Akwai kotu da za ka kai kara har zuwa kotu ta karshe, daga ita sai hakuri da rungumar kaddara.”

Wannan shi ne fatan yawancin Amurkawa da duniya baki daya wadanda ke kallon dimukradiyyar kasar abar kwaikwayo, da suke fatan dorewarta.