Atletico na kwaɗayin Garnacho, Man Utd na son riƙe Diallo

Alejandro Garnacho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Atletico Madrid na duba yiwuwar saye ɗan wasan Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20. (Fichajes - in Spanish)

Manchester United ta yi nisa a tattauna cimma yarjejeniyar tsawaita zaman Amad Diallo mai shekara 22 daga Ivory Coast. (ESPN)

Kocin Roma Claudio Ranieri ya ce ɗan wasan gaba Paulo Dybala, mai shekara 31, na iya barin ƙungiyar idan ba ya jindadin zaman, wannan ya biyo bayan tattaunawar wakilansa da Galatasaray. (Corriere dello Sport - in Italian)

Manchester United na iya gwadawa RB Leipzig kwanji a dauko ɗan wasan Paris St-Germain da Faransa, Randal Kolo Muani mai shekara 26, a matsayin ɗan aro. (Football Insider)

Chelsea da Aston Villa da Stuttgart da kuma Newcastle na kwaɗayin ɗan wasan PAOK da Girka Stefanos Tzimas, mai shekara 18 da ke zaman aro a Nurnberg. (ESPN)

Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Southampton da kocin Sheffield, Danny Rohl kan kujerar horaswa a St Mary. (Sky Germany)

Saints na kuma duba yiwuwar dauko kocin West Brom, Carlos Corberan. (Sky Sports)

West Ham na farautar mai tsaron raga daga Freiburg Noah Atubolu, ɗan shekara 22. (Fabrizio Romano)

Burnley ta yi nisa a tattauna sayen ɗan wasan Peru Oliver Sonne, mai shekara 24, daga Silkeborg a yarjejeniyar fam miliyan 2 da rabi. (Football Insider)

Tsohon kocin Birmingham City da Millwall Gary Rowett na tattaunawa da Oxford United. (John Percy/Telegraph)

Barcelona ta gargadi ɗan wasan baya a Uruguay Ronald Araujo, mai shekara 25 da kuma mai buga tsakiya daga Netherlands, Frenkie de Jong, mai shekara 27, kan su sa hannu a sabon kwantiragi da ƙungiyar ko su fuskanci sauyin matsuguni. (Sport - in Spanish, external)

Everton na sa ido kan ɗan wasan nan mai shekara 22 daga Rangers da Morocco, Hamza Igamane, yayinda take cikin rashin tabbas kan ƴan wasanta na Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 27, da Beto, mai shekara 26 daga Portugal. (TBR Football, external)

Juventus na kitsa sayo ɗan wasan Feyenoord da Slovakia, David Hancko, mai shekara 27. (Calciomercato - in Italian, external)