Mudryk na Chelsea ya gaza tsallake gwajin shan ƙwaya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Sean Kearns
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
Ɗanwasan gefe na Chelsea Mykhailo Mudryk ya ce ya "kaɗu matuƙa" bayan gwaji ya nuna cewa yana ɗauke da sinadaran wata ƙwaya da aka hana 'yanwasa sha.
A ranar Talata kulob ɗin ya sanar cewa hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila Football Association (FA) ta tuntuɓe su bayan "wani sakamako da aka gano a gwajin fitsari" da aka ɗauka na ɗanwasan na ƙasar Ukraine.
Mudryk ya musanta zargin cewa ya yi amfani da sinadarin da gangan, amma Chelsea ta ce za ta shiga aikin gano abin da ya faru.
"Abin ya zo da mamaki sosai saboda ban taɓa yin amfani da wannan sinadari da aka hana ba da gangan, ko kuma karya wata doka, kuma ina aiki tare da kulob ɗina domin binciken ta yadda aka yi hakan ta faru," kamar yadda Mudryk ya wallafa a Instagram.
"Na san cewa ban aikata wani laifi ba kuma ina fatan zan dawo taka leda nan gaba kaɗan."
A ƙarƙshin dokokin FA, za a iya dakatar da 'yanwasa daga taka leda idan suka gaza tsallake gwajin shan ƙwayoyin da aka haramta.
Sai dai kuma, da BBC Sport ta tuntuɓi FA ba ta tabbatar ba ko an dakatar da Mudryk mai shekara 23 da kuma lokacin da aka yi gwajin.
Duk ɗanwasan da aka samu da karya dokar da gangan, za a iya dakatar da shi tsawon shekara huɗu kamar yadda dokokin Fifa suka tanada.
Mudryk bai buga wa Chelsea wasa biyar da suka gabata ba, amma mai horarwa Enzo Maresca ya ce rashin lafiya ce ta sa babu shi a cikin tawagar a yanzu.
Ya ci wa Chelsea ƙwallo 10 cikin wasa 73 da ya buga tun bayan komawarsa Ingila daga Shaktar Donetsk ta Ukraine kan fam miliyan 89 a 2023.










