Inter ta zazzaga wa Lazio ƙwallayen da ba a taɓa zuba mata ba har gida

Marcos Thuram

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mai riƙe da kofin gasar Serie A, Inter Milan, ta zazzaga wa Lazio 6-0 har gida kuma ta kafa mata tarihin yawan ƙwallayen da ba a taɓa zuba mata ba a gidanta a tarihi.

Lazio ta fara wasan na daren jiya ne da maki iri ɗaya da na Inter, tazarar maki shida tsakaninsu da Atalanta da ke jagorantar teburin gasar, amma ta kasa cin ƙwallo ko ɗaya a wasan.

Ba a ci Lazio ba cikin wasa 12 da ta buga a gida, kuma ba su yi rashin nasara ba gaba ɗaya tun daga watan Maris. Su ne kuma a saman teburin gasar Europa.

Hakan Calhanoglu ne ya fara ci wa Inter ƙwallo a minti na 41 daga bugun finareti. Sai Federico Dimarco ya ƙara kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Nicolo Barella ne ya ci ta uku bayan minti shida da dawowa, kafin Denzel Dumfries ya ƙara minti biyu bayan haka. Carlos Augusto da Marcus Thruam ne suka rufe taron da nasu ƙwallayen.

Inter ta ci gaba da zama ta uku a teburin Serie A da makinta 34 cikin wasa 15, yayin da Atalanta ta ɗaya a teburin ta ba ta tazarar maki uku, amma kuma tana da kwantan wasa ɗaya.

Lokaci na ƙarshe da aka ci Lazio 5-0 a gida shi ne a 1959 a wasa da Fiorentina.