Aston Villa na fatan raunin da Konsa ya ji ba mai muni bane

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa na fatan raunin da Ezri Konsa ya ji ba wani mai muni bane a karawar FA Cup da Tottenham a zagaye na huɗu ranar Lahadi.
Ɗan wasan tawagar Ingila ya ji rauni tun kan hutu a wasan da Villa ta kai zagaye na biyar a FA Cup, sakamakon nasara doke Tottenham da cin 2-1.
Karon farko da Villa ta kai irin wannan matakin, bayan 2014/15, tana sa ran yin abin kirki, bayan da tuni aka yi waje da Arsenal da Chelsea da kuma Liverpool daga gasar.
Konsa zai bi sawun masu jinya a Villa Park, idan likitoci suka tabbar da raunin da ya haɗa da Boubacar Kamara da kuma Lamare Bogarde.
Ana sa ran Axel Disasi sabon ɗan ƙwallon da ta ɗauka a Janairu, zai yi mata gasar Premier League ranar Asabar da za ta kara da Ipswich Town.
Aston Villa wadda ta kai zagaye na biyu a Champions League kai tsaye, tana ta takwas ɗin teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 37.
Ƙungiyar ta Villa Park ta ci wasa 10 da canjaras bakwai da rashin nasara bakwai a wasa 24 da ta yi a Premier League kawo yanzu.







